Connect with us

LABARAI

Kungiyar Mata Injiniyoyi Za Ta Gina Dakin Karatu A Misau

Published

on


Kungiyar Mata Kwararrun Injiniyoyi ta Kasa ‘Association of Professional Women Engineers of Nigeria’ (APWEN) za ta gina dakin binciken Ilimin zamani hade da sanya kayyakin aikin zama a ciki a  gami da daukar dawainiyar karatun yara mata su goma tun daga matakin Firamare har zuwa ga kammala jami’a a karamar hukumar Misau da ke jihar Bauchi kyauta.

Wannan dakin binciken ilimin wanda za kawatasa da kayyakin bincike na zamani, za a yi masa ginin ne cikin salon zamani wanda za a gina a makarantar Firamare ta Central Primary School, da ke karamar hukumar Misau, Bauchi.

Shugaban kungiyar matasa Injiniyoyi ta kasa, (APWEN) Engineer Felicia Nnenna Agubata ita ce ta shaida hakan a sa’ilin da take aza tubalin fara aikin dakin nazarin ilimin a Firamaren Central Primary School da ke Misau a karshen makon nan.

Ta bayyana cewar hakan na daga cikin shirinsu na  inganta rayuwar mata kan fannonin ilimin kimiyya da na Injiniyaci tun daga matakin farko ne.

Ta ce; “Domin mu samu nasarar shawo kan matsalolin rashin samun mata a fannin Injiniyanci da kuma shuwagabani,” In ji Felicia Nnenna Agubata

Ta kuma shaida cewar a kowanne bigire suka samu dama suna kokarin fadakar da mata musamman yara kanana masu tasowa kan su rungunmi fannin Ininiyanci domin kyautata wa mata rayuwarsu ta kowace fanni.

Ta yi nuni da cewar mata suna kaurace wa shiga sha’anin Injiniyanci wanda kuma hakan sam bai dace ba, tana mai amanar cewar mata suna da gagarumar rawar tawa wajen ci gaba ta wannan sashin na Injiniyanci.

Injiniya Nnenna ta bayyana cewar tallafin karatun wacce za a gidana dakin binciken a wannan yankin na Misau ya samu ne daga aljihun babban shugaban sashin hukumar albarkatun danyen man fetur ta kasa (GMD NNPC) Injiniya Maikanti Kachalla Baru.

Felicia Nnenna Agubata ta kara da cewa, “Wannan dakin nazarin ilimin wacce za a gina a kuma sanya mata na’urorin zamani na su kwantafuta, littafai binciken ilimin kimiyya, da sauran muhimman kayyakin da suka dace na zamani da kuma fasaha,” In ji Felicia.

Injiniyar ta kuma bukaci iyaye da su karfafi karatun ‘ya’yansu mata ta fuskokin nazarin lissafi, kimiyya da kuma na fasaha, ilimin sinadarai, da kuma uwa-uba ilimin Injinanciya wacce ta bayyana cewar mata sun yi matukar karanci a wannan sashin.

Da yake nashi jawabin, shugaban sashin danyen man fetur ta kasa, Maikanti Kachalla Baru, ya jinjina wa kungiyar mata Injiniyoyi a bisa daura sa a wannan hanyar inganta rayuwar matasan.

Ya bayyana cewar da zarar yara mata suka samu karfafawa da wayar musu da kai tun daga matakin firamare kan su sanya hankulansu wajen ilimin kimiyya da fasaha tabbas za a samu gagarumar sauyi kan masu kin kasancewa a irin kwasa-kwasan.

Baru ya ce, “Ilimin Injiyanci hanyace ta ci gaban kasa, don haka za mu ci gaba da karfafa matasa musamman mata kan wannan fannin domin a samu gagarumar sauyi a ciki,” In ji shi.

Da yake jawabin godiya a madadin jama’an Misau baki daya, Sarkin Misau Ahmed Suleiman ya gode ne wa kwararrrun mata Injiniyoyin a bisa kawo wannan gagarumar dauki wa jama’ansa.

Haka zalika, an baiwa shugaban sashin mai NNPC Boss, Maikanti Baru, da Sarkin Misau Emir of Misau Ahmed Suleiman, lambar yabo gami da gayyatarsu don kaddamar da fara wannan aikin gina dakin binciken wanda ake sa ran kammalasa nan ba da jimawa ba.


Advertisement
Click to comment

labarai