Connect with us

SIYASA

Gwamnatin Badaru Na Kyautatawa Ci Gaban Matasan Jihar Jigawa –Alhaji Salisu

Published

on


Zan Gudanar Da Ingantaccen Mulki A Sakkwato -Faruku Yabo

Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Babban Jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Honarabul Faruku Malami Yabo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a zaben 2019 da ke tafe tare da alwashin bunkasa Jihar da al’ummarta.

“A shekarar 2014 na kasance cikin masu neman takarar Gwamna. A zaben 2019 da ke tafe da yardar Allah zan kasance dan takarar kujera mafi daraja ta daya a Sakkwato. Ina neman addu’a da cikakken goyon bayan Sakkatawa domin samun nasarar mu nasarar ku ce bakidaya.” Ya bayyana.

Tsohon Kwamishinan na Kudi da Lamurran Kananan Hukumomi a zamanin Gwamnatin Wamakko ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wajen bukin kaddamar da ofishin musamman na tsara shirye-shirye mai suna WAFEEPRO Studio a Sakkwato mallakar fitacce kuma kwararren dan jarida Wafee Ahmadu-Suka.

“Tsayawa ta takara a 2019 babu gudu babu ja da baya. Da yardar Allah za mu kafa Gwamnatin jama’a ta jama’a domin jama’a wadda za ta mutunta jama’a wadda kuma za ta bada fifiko wajen shimfida ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma.” In ji shi.

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar an jima a na rade-radin Yariman na Yabo wanda babban makusanci ne ga babban uban jam’iyyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Wamakko zai shiga cikin masu neman shugabancin Jihar Sakkwato a zaben 2019 ta yadda a yanzu hasashen ya tabbata a karshen mako. “Za mu jira zuwa lokacin da dokar kasa ta bada damar fara gangamin harkokin siyasa.” Ya tabbatar.

A taron wanda jigogin APC kuma manyan na hannun daman Sanata Wamakko suka halarta, Basaraken na Masarautar Yabo ya jaddada cewar babu wata Dimokuradiyya a Duniya da za ta samar da ci-gaba idan ba a baiwa ‘yan jarida cikakkiyar dama ba.

Ya ce assasa gidajen Radiyo masu zaman kansu da a ka yi a Sakkwato za su taimaka kwarai wajen samar wa jama’a ‘yanci tare da yayata ra’ayoyin su. A kan wannan dan takarar ya bayyana cewar ‘yan jarida abokan sa ne don haka zai gudanar da Gwamnatin da ba za ta kyamaci ‘yan jarida ba.

Yabo wanda ya kaddamar da dakin tsara shirye-shirye na Wafeepro ya bayyana cewar zai jagoranci samarwa masana’antar masu zuba jari tare kuma da bayyana cewar nan ba da jimawa ba ofishin zai zama gidan Talbijin mai watsa shirye-shiryen akwatunan talbijin ta tauraron Dan-Adam.

Yariman Yabo wanda a nan take a wajen ya nada Wafee Ahmadu Suka a matsayin Mashawarcinsa na Musamman kan Yada Labarai ya bayyana tsohon dan jaridar a matsayin kwararre kuma gogagge a aikin yada labarai wanda jama’a za su ci-gaba da amfana da dimbin basira da hikimarsa ta aikin yada labarai a tsayin shekaru da dama. “Daga yanzu Wafee Suka zai kasance mai kula da dukkanin harkokina na yada labarai.” Ya ayyana.

Tun da fari a jawabinsa Tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Rima, Wafee Ahmadu-Suka ya bayyana cewar ya assasa ofishin na tsara shirye-shirye domin bada gudunmuwa ga aikin yada labarai da kafafen yada labarai domin su gudanar da aikin su a mataki na kwararru.

Ya ce sun tanadi dukkanin na’urorin da za su iya gogayya da dukkanin gidajen radiyo masu karamin zango. “Akwai dama yanzu sosai ga ‘yan jarida a Sakkwato domin su samu kwarewar da ta kamata.” In ji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai