Connect with us

KASUWANCI

Fasahar Zamani: Shugaban Bankin Duniya Ya Shawarci Kasashen Afrika Kan Habbaka Tattalin Arziki

Published

on


Shugaban Bankin Duniya, Mista Jim Kim, ya bukaci kasashen Afrika da su bunkasa sassan tattalin arzikin su ya zuwa masu amfani da kimiyyar fasahar zamani, su kuma gaggauta samar da ci gaban na su a fasahar kimiyyan zamani domin gujewa rasa milyoyin ayyukan yi.

Kim, ya bayar da wannan shawarar ce ranar Alhamis a Washington DC, sa’alin tattaunawar sa da manema labarai lokacin bude tarukan shekarar 2018 na cibiyar lamuni ta duniya IMF, da kuma Bankin Duniya.

A cewar shi, hakan ya zama wajibi domin yawancin tattalin arzikin duniya yanzun duk a kan fasahar zamanin take tafiya, ga kuma yawaitan fasahar amfani da na’urar, 3D, mutum-mutumi da kuma dubarun zamani wanda dan adam ya kirkira.

“Mun damu sosai kan yadda yawancin kasashen na Afrika ba su nu na wani hobbasan tafiya da tsararrakin su ba a wannan sashen na tattalin arziki. Akwai kuma shaidu kwarara da ke tabbatar da ayyukan masu yawa da mutane ke yi da hannun su, duk nan ba da jimawa ba, fasahar zamanin za ta kwace su.

“Muna fatan fasahar zamanin za ta taimakawa kasashe da yawa na Afrika domin su bunkasa, su kuma sami sabbin hanyoyin tafiyar da tattalin arzikin na su.

Kim, ya kuma shawarci Nijeriya da sauran kasashen na Afrika da su zuba jari mai yawa a sashen ilimi, wanda a cewar sa, shi ne kadai hanyar da za su ci gajiyar bunkasa tattalin arzikin na su ta hanyar fasahar ta zamani.

“Ba tare da ilimin da ya cancanta ba, kasashen na Afrika ba za su san komai ba, nan gaba kuma ba abin da za su amfana da shi. Muna da tabbatacciyar shaida a kan hakan. Matukar akwai barazanar rashin ilimin da ya kai kashi 30 ko ma kashi 50, to duk wadannan yaran ba abin da za su sani na fasahar ta zamani a nan gaba. Don haka tilas ne a zuba jari sosai kan samar da masu ilimin.

Ya kuma yi tsawa ga kasashen na Afrika da su habaka hanyoyin su na tara haraji su kuma kara yawan sassan samar da kudaden shigar su a gida da za su gina manyan ayyuka da su, kamar makarantu, asibitoci da hasken lantarki.

“Muna ganin kamata ya yi akalla kasashen na Afrika, kashi 15 na kudaden shigan su su kasance a cikin gida ne suke tara su, hatta Nijeriya, Ba ta yin hakan. Ya kuma kamata kasashen na Afrika su cire duk wani tallafin mai, wanda a cewar sa, mawadata kawai tallafin ke kara wadatawa fiye da talakawa.

“Hatta tallafin Noma da suke bayar wa, kusan duk ba su da amfani. Don ba sa taimakon kananan manoma. Kamata ya yi kuma su kara yawan harajin da suke karba kan taba sigari don su kara yawan kudin shigan su, su kuma rage shan tabar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai