Connect with us

LABARAI

Ban Taba Mallakar Naira Biliyan Daya Ba A Rayuwata –Wamakko

Published

on


Tsohon Gwamnar Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewar a rayuwarsa bai taba mallakar tsabar zunzurutun kudi har naira biliyan daya ba.

Wamakko wanda shine Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa ya bayyana cewar mulkin da ya gudanar na tsayin shekaru takwas 2007-2015 ya himmatu ne wajen shimfida ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma ba satar kudaden jama’a ba kamar yadda wasu ke ikirari.

Babban jigon na APC wanda ke wakiltar Mazabar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa ya bayyana hakan ne a yayin mayar da martani ga rahoton da kafafen yada labarai suka wallafa cewar EFCC na bincikensa da shi da Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran Akidar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan batan dabon naira biliyan 18 a lokacin da suke kan gadon mulki.

Ya ce “An ce a na zargin Kwankwaso da batar da biliyan uku ni kuma bilyan 15. Ina son jama’a su sani ba Hukumar EFCC ce ta fitar da rahoton ba. Labari ne na karya aka tsara wanda ba ya da tushe ballantana makama.”

Sarkin Yamman na Sakkwato ya ce “Wane irin mahaukaci ne ko shashasha ne zai saka kudi har naira biliyan daya a cikin asusun ajiyarsa? Ai wannan ma ya wuce hauka kuma EFCC hukuma ce wadda ta san abin da take yi da irin kalaman da za ta yi ko da kuwa ta na binciken mutum.” In ji Wamakko.

Ya ce EFCC hukuma ce mai kima da martaba wadda ke da jami’ai da ke da dattako wadanda ba za su taba amfani da kalaman cin zarafi kwatankwacin wanda aka wallafa a jaridun ba. “A shirye muke a kodayaushe mu gabatar da kan mu kan kowane irin bincike daga kowace irin hukumar binciken cin hanci da rashawa a matsayinmu na ‘yan kasa masu bin doka.”

Sanatan wanda yana daya daya cikin Gwamnonin da suka yi fito-na-fito da Gwamnatin Jonathan ya bayyana cewar ko kadan bai fi karfin doka ba amma idan za a yi bincike to a yi shi yadda ya kamata ba wai a rika yayata labaran kanzon kurege ba. “Idan da kudi muke so ai da mun bi Jonathan amma maimakon hakan da ni da wasu Gwamnoni mun fito fili mun kalubalance shi.” Ya jaddada.

A rahoton an bayyana cewar EFCC ta na zargin Wamakko da Sanata Kwankwaso da salwantar da tsabar zunzurutun kudi har naira bilyan 18. 08 a lokacin da suke kan mulki.

Binciken Sanatan kuma babban jigo a Jam’iyyar APC kamar yadda rahoton jaridu ya nuna ya biyo bayan korafin da EFCC ta samu daga wata kungiya mai suna Mobement for the Liberation and Emancipation of Sokoto State wadda ta zargi Tsohon Gwamnan da yi wa bilyan 15 hadiyar kafino.

Surajo Sa’idu da Mudassir Umar Alhassan ne suka rattabawa takardar koken hannu wadda ke dauke da kwanan wata 10 ga Agusta 2015. Kungiyar ta zargi Wamakko wanda ya yi mulkin Jihar Sakkwato daga 2007 zuwa 2015 da karkatar da kudaden da ya kamata ya yi wa jama’a ayyukan ci-gaba zuwa aljihunsa.

Wamakko dan shekaru 65 ya bayyana cewar “Ban taba mallakar naira biliyan daya ba a rayuwata ba. Ni ba mai kudi ba ne kuma ba na ajiye kudi. Jama’ar Jihar Sakkwato sun san abin da na yi masu da kudin su a mulkin tsawon shekaru takwas. Ina kalubalantar masu koken da idan ina da wadannan kudaden a dauko su a buga a jarida domin jama’a su gani. Idan har an wallafa to na yadda babu wata jayayya.” Ya bayyana.

Ya bayyana cewar wadanda suke da alhakin fitar wannan labarin suna karkashin wani dan siyasa ne wanda ke son ganin bayansa wanda ke ganin me yasa Wamakko yake raye.

“Ya yi koken ba mu yi jami’a mallakar jiha ba kuma EFCC ta zo ta bincika ta ga jami’ar da muka gina wadda kuma ita ce ta farko a kasar nan da ta fara karatu a mazaunin ta na din-din-din har dalibai rukunin farko sun tafi Hidmar Bautar Kasa, ya ce babu gidaje 500 na Kalambaina, an zo an duba an ga gidajen, hasalima Shugaba Buhari ne ya kaddamar da su, ya sake cewa rukunin gidaje na Mana yaudara ce su ma an zo an ga gidajen, ya ce mun siyar da hannun jari shi ma an bincika an ga har mun nunnunka hannayen jarin.” In ji Sanatan.

“A mulki na, na kwatanta adalci tare da rike amanar dukiyar al’umma. Na gina manyan makarantu guda biyar ciki har da jami’a mallakar jiha irinta ta farko a kasar nan wadda ta fara karatu a cikin mazaunin ta na din-din-din. Na gina gidaje dubu 5, 000 na shimfida hanyoyi sama da kilomita dubu 1, 000, na kuma shimfida titunan kilomita biyar, biyar a dukkanin Kananan Hukumomi 23 da ke a wannan Jihar.” Ya bayyana.

Ya kara da cewar “Na kuma gina Manyan Asibitoci a dukkanin Kananan Hukumomi 23, yayin da kowace mazaba daga cikin mazabu 244 da muke da su suka samu Asibitin Kiyon Lafiya a Matakin Farko (PHC) masu dauke da gadon kwana rukuni na biyu da motar tafi da gidanka tare da daukar ma’aikata da kuma gina gidajen ma’aikata. Baya ga wannan na nunka hannayen jarin da na tarar ninkin ba ninkin, na kuma sayi sabbin hannayen jari har miliyan 20. Na karfafawa matasa sama da dubu 500 a shiraruwa daban-daban. Na shimfida tagwayen hanyoyi na Gabascin Sakkwato da hanyar filin jirgi kuma har na sauka mulki babu ma’aikacin da ke bina bashin naira daya domin mun biya albashi har zuwa 29 ga Mayu.” In ji shi.

Wamakko wanda ya bayyana cewar yana cikin Gwamnoni na farko da suka fara biyan tsarin albashi mafi kankanta na 18, 500 ya bayyana cewar akwai Gwamnonin da ake bin su bashin albashin watanni dai-dai har shida.

Sanatan wanda Mai Martaba Sarkin Daura Umar Faruk Umar ya baiwa sarautar Marafan Hausa ya bayyana cewar idan har watakila wadanda suka tsara labarin sun yi ne domin nunawa duniya cewar a siyasance ba ya tare da Shugaba Buhari to sun yi kuskure domin dangantakarsa da Buhari kyakkyawa ce domin a cewarsa Buhari abokinsa ne kuma bai taba fada da Buhari ba, suna kuma haduwa suna tattaunawa.

Wamakko ya bayyana cewar ya rarraba sama da motoci dubu 10, 000 da babura dubu 75, 000 a matsayin bashi. Ya kuma ce ya karfafawa dubban daruruwan ‘yan kasuwa da manoma da bashin bilyoyin naira daga 2007-2015.

“A lokacin da na shiga ofis, dalibai dubu 6, 000 ne ‘yan asalin wannan jiha ke yin rajistar rubuta jarabawar shiga jami’a ta UTME a kowace shekara amma adadin ya karu zuwa sama da dubu 35, 000 a shekaru hudu na farko na mulki na.”

Sanata Wamakko ya bayyana cewar bai barwa Magajinsa bashi ba kuma bai taba zama wajen Jiharsa sama da mako daya ba. Ya ce a shekaru takwas da ya yi yana mulki sau daya kacal ya taba zuwa Kasar Amurka ita din ma ya je ne a bisa gayyatar Gwamnatin Kasar haka ma ya ce a matsayinsa na Gwamma sau daya kacal ya je Kasar Ingila a lokacin da ya gabatar da lacca a Chatham House kamar kuma yadda ya ce sau daya ya ke zuwa Kasar Saudiya a kowace shekara domin gudanar da Ibadar Umra.

Wamakko ya bayyana cewar al’ummar Jihar Sakkwato amana ce a gare shi kuma sun san ya kwatanta sosai a mulkin sa shi yasa suka nuna masa kaunar da ba su taba nunawa wani mahaluki ba.


Advertisement
Click to comment

labarai