Connect with us

RAHOTANNI

Al’umma Na Farin Ciki Da Shirin Gwamnatin Jihar Katsina Na Farfado da Harkar Noma

Published

on


Manyan manoma na yankin Dungun Mu’azu dake karamar hukumar Sabuwa ta jhar Katsina sin nuna farin cikinsu a kan irin aikace-aikace da shirye shiryen da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari ke domin farfado da kara karfafa harkan noma a fadin jihar, wani hamshakin manomi mai suna Alhaji Umaru Bakaja Da Hukuma ne ya  bayyana haka a yayin da yake tattauna da wakilinmu bayan sun kammala wani taro a garin Dungun Mu’azu.

Alhaji Umaru Bakaja Da Hukuma wandan shirye shiryen da gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ta kirkiro musamman shirin bayar da takin zamani ga manoma a kan lokaci da kuma tallafa musu da bashin kudade zai matukar taimaka wa kokarin da akeyi na bunkasa samnar da abinci a cikin jihar dama tarayyar Nijeriya baki daya, daga nan ya bukaci sauran gwamnatocin jihohi da suyi koyi da tsare tsaren gwamnan jihar Katsina a fannin mona, “Yin haka zai tallafa wa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na ganin kasar nan ta dogara da kanta wajen ciyar da ‘yan kasa har a samu rarar da za a fitar kasashen waje” inji shi.

Daga nan Alhaji Umaru Baka Ja da Hukuma ya bukaci gwamnati da ta rinka ware kason manyan manoma a yayin da ake rabon takin zamani da sauran kayan aikin noma, “ya kamata a rinka la’akari da tsananin bukatar da manyan manoma suke das hi na kayan noma wajen rabon da ake yi”

A nasa tsokacin Alhaji Shitu Mai Manja, wanda shi ma yana daya daga cikin manyan manoman karamar hukumar Sabuwa, ya bukaci gwamnati data kara kaimi wajen samar da tsaro a yankin karamar hukumar Sabuwa, musamman a dazukan Birnin Gwari, “rashin tsaro na hana wasu manyan mano noma dukkan gonakinsu, abin kuma dake kawo cikas wajen yawan hatsin da ake girba a wannan yankin” inji shi. Daga nan ya bukaci manoma a yankin dasu yi aiki tukuru su kuma rungumi duk wani tsari na ci gaba da gwamnati ta fito da shi.

Da yake nasa tsokacin, wani babban manomin masara mai suna Alhaji Surajo ya ce, in har manoma zasu samu tallafi da kwarin gwiwar daya kamata, to lallai za a samu cikakken abin da zai ciyar da al’ummar kasar nan har a samu a ciyar da kaashe makwabta, daga man ya bukaci manoman da suka karbi bashin banki su gaggauta biyan bashi da ake bin su, “Yin haka zai ba gwamnati karfin gwiwar kara fito da wasu tallafin” ya kuma bukaci gwamnati data tanidi kudade domin sayen hatsi daga manoma domin sayar wa mabukata a lokacin da hatsin ya yi tsada.

 


Advertisement
Click to comment

labarai