Connect with us

LABARAI

Sabon Katafaren Shago A Hajji Camp Zai Rage Wa Matasa Zaman Banza –Aminu Algazari

Published

on


An bayyana cewa, sabon katafaren shagon sayar da kayayyaki da a ka bude a zangon alhazai (Hajji Camp) da ke birnin Kano zai rage zaman banza tsakanin matasa, in ji babban dan kasuwa, Alhaji Aminu Algazari.

A wannan makon ne daya daga cikin matasan ‘yan kasuwar Haji-kam da ke kusa da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya bude wata katafariyar ginin filaza wanda ya cika shi da kaya kala-kala. Da ma ita wannan kasuwa ta yi suna wajen saida kayan kasar Saudiyya da ma na wasu kasashe.

Ganin haka ne wannan dan kasuwar, Alhaji Algarzali, ya yi ta-maza wajen samar da kaya, domin saukakawa al’umma, duk da kukan rashin kudi a hannu al’umma bai hana samar da irin wannan wurare ba.

Ranar Larabar nan da ta gabata ne a ka bude wannan katafaran guri. Wakilinmu ya sami ganawa da Alhaji Aminu Algazari, inda ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bada damar da har wannan guri ya samu.

“Na farko dai samar da wannan guri shi ne zance wannan ikon Allah ne, abu na biyu kuma mu samar da aiki ga matasa, domin wannan lokaci sai an tallafawa juna za mu ke ganin sauki tsakaninmu. Kuma mun yi ragi ga duk mai son kaya a wannan babban guri, mun yi ragi na musamman.”

Ya kara da cewa, “to, gaskiya wannan abu ne mai kyau da yakamata masu hannu da shuni su dukufa wajan bude gurare irin wannan domin rage zaman banza, domin idan ka dubi matasa yanzu sunyi yawa babu abunyi ko ina aikata manyan lefuka sunyi yawa. Ina amfani da wannan damar wajan kira ga gwamnati data cigaba da kokari wajan samarwa da matasa aikinyi munsan a na kokari to amma akara akan nada.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai