Connect with us

LABARAI

PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 –Mariya Waziri

Published

on


Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta yi alkawarin bai wa mata karin manyan mukamai, idan har su ka fito su ka zabe ta ta lashe babban zaben kasa na 2019. Hakan ya fito ne daga bakin shugabar matan jam’iyyar ta kasa, Hajiya Mariya Waziri, ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da ta ke gana wa da shugabannin matan jihohi na PDP a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja.

Hajiya Waziri ta kuma yi kira ga shugabannin mata da su koma jihohinsu gaba-gadi su janyo hankalin matan jihohinsu kan shirin da PDP ke yi samar mu su da ayyukan yi matukar Allah Ya nufa jam’iyyar ta dawo kan kujerar mulkin Nijeriya a 2019.

Sai ta yi kira ga matan da su fito takara a matakai daban-daban na siyasa, domin a rika damawa da su, ta na mai jan hankalinsu da su yi kokarin ganin a 2019 an sami mata gwamnoni a wasu daga jihohin kasar.

Don haka sai Waziri ta ce, tilas ne mata su hada kansu waje guda su zabi PDP, don fitar da su da matasa ’ya’yansu da ma mazajensu daga kuncin da jam’iyya mai mulki, APC, ta jefa su a ciki. Sai ta kara da cewa, lallai ne su bazama jihohi su tabbatar da cewa, mata sun adana kuri’unsu, domin ta hanyar hakan ne kadai za su iya yiwa APC korar kare daga fadar shugaban kasa.

Shugabar matan PDP din ta kasa ta kuma ce, ba mukamin shugaban kasa ko gwamnoni kadai matan za su nema ba, a’a, ya wajaba su tsaya takara a sauran mukamai kamar na sanatoci, majalisar wakilai da jihohi da sauransu, domin bai wa mata ’yancinsu da taimaka mu su kan tafarki mai kyau na daga cikin akidar PDP.

 


Advertisement
Click to comment

labarai