Connect with us

LABARAI

Matasan Najeriya Ba Malalata Ba Ne –Fadila Tilo

Published

on


Wata Matashiyar yar Najeriya yar asalin jihar Katsina Hajiya Fadila Sani Tilo, ta mayar da martani ga kalaman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda yace mafi yawan Matasan Najeriya cima zaune ne malalata ita kuma ta ce matasan ba cima zaune bane.

Hajiya Fadila Sani Tilo, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da LEADERSHIP A Yau Lahadi, cewa kamata ya yi a jinjinawa matasan musamman yan arewa saboda yadda suke fadi tashin neman na kansu domin duk wani lungu da sakon da kabi zaka ga matasa sun tashi suna neman yadda za su tsira da mutuncin su.

A cewar ta yanzu a arewacin Najeriya duk inda ka shiga za kaga matasa na tura baro wasu na Baban Bola wasu na Tura ruwa da sauran nau’ukan aikin karfi dan neman halak din su to a na menene za’a kira matasan da cewa su cima zaune ne su.

Kasancewar Muhammadu Buhari shugaban kasa watakila batun da ya yi wasu tsiraru ya gani irin masu macecciyar zuciyar nan da suke bin kan ’yan siyasa wadanda ba za’a rasa ba suke bangar siyasa ya furta wannan kalamai akan su idan haka ne kuma bai kamata ya yi jam’i yace matasan Najeriya malalata bane kuma cima zaune ba.

Hajiya Fadila Sani, tace idan irin wannan aikin da matasan ke yi na karfi bai gamshe shi ba to ya samar musu da aikin da ya dace tunda a lokacin da yake yakin neman zabe a shekarar 2015 ai ya bayyana cewa zai samarwa da matasan aikin yi me ya hana ya cika wannan alkawarin yanzu har ya ke kiran matasan da Malalata.

Ta kuma yi kira game da bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawarin cewa idan ba zai iya samarwa da matasan nan ayyukan da za su yi ba kar ya kira su cima zaune domin wani ma sana’ar faci ya ke yi wani Makanikanci da haka kuma yake rike da iyalansa wanda da basa wannan sana’ar da su ne zai sa a kirasu cima zaune amma ta ya ya mai sana’a ko wanda yake da aikin yi za’a kira su malalata.

Haiya Tilo, ta kara da cewa watakila matasan da shugaban kasa Buhari ya ke kira malalata din irin wadancan yan bangar siyasar ne da suka kashe zuciya suke bin kan yan siyasa wanda kuma duk yadda kayi da samarwa mutane aikin yi wasu ba za su yi saboda sun saba da karbar na banza.

Sannan ta ce a dangane da wannan kalaman na shugaba Buhari na kiran matasa cima zaune ya sake komawa kafar yada labarai ya bai wa matasan hakuri saboda ya wanke kansa dan a gaskiya matasa ba malalata bane kamar yadda yake fadi.

Daga nan sai Hajiya Fadila Tilo, tace saboda yadda matasan Najeriya ke jajircewa wajen neman na kansu da fadin tashin da suke yi dan rufawa kansu asiri kamata ya yi gwamnati ta bai wa matasan lambar yabo, domin baya ga sana’aoi da suke ai shi Buharin ya sani a lokacin sa ne matasan da dimbin yan Najeriya suka koma gona.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai