Connect with us

LABARAI

Mariri Ya Sha Alwashin Daukar Matasa Aiki

Published

on


Ganin yadda Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke da burin ganin bunkasar Masana’antu a Najeriya da kuma karfafawa Yan Kasuwa na su bunkasa Masana’antun su da suka mallaka kamar yadda doka ta tsara a wannan lokaci ganin haka ne Alahji Yusuf Mariri shugaban Masana’antar fasa dutse ta Kujama yayi alwashin daukar Ma’aikata Matasa domin dai rage masu zaman kasha wando da rashin aikin yi a kasan nan.

Shi kuwa Barista Safiyanu Sale Gadau wanda shi ne mai kula da al’anuran Shari’a da tabbatar da duk wata yarjejeniya ta mallaka na Masana’antar Fasa Dutse ta kujama ya bayyana cewa babu wata matsala ga dukkan wani dan kasa ya mallaki abin da doka ta yarje masa bisa tsari da dokokin kasa suka amince musamma ma a wannan lokaci da Gwamnatin Tarayya ke kokarin ganin mutane sun mallaki Masana’antu domin farfado dasu dan samawa Matasa aikin yi.

Shi ma jigo kuma Darkta a wannan Masana’anta ta fasa dutse Alhaji Sunusi Usman ya ce burin su wannan Masana’anta da kujama su a yanzu za su yi duk wani abu da ya kamata wajan ganin ta cigaba domin tabbatar da samawa Matasa aiki yi ta hanyar kula da wal wala dan jin dadin su.

Tun da farko a nasa jawabin wanda ya wakilci Daraktan kula da cefanar da kadarorin Gwamnatin Tarayya ya ce burin shugaban kasa ne a samu cigaba ta fuskar Masana’antu a kowanne sashi dan haka yayi kira ga al’ummar Najeriya da kuma makusanta ta wannan Masana’antu da su cigaba da bin doka da oda ta hanyar zaman lafiya da al’umma a wanann lokaci.

 


Advertisement
Click to comment

labarai