Connect with us

LABARAI

2019: Kwankwasiyya Ta Raba Wa Mata 100 Naira 10,000 A Yobe

Published

on


Kungiyar kwankwasiyya a karkashin tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso wadda a yanzu shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tsakiyar Kano a majalisar dattijai ta kasa ta kai tallafin kudade Naira 10,000 ga mata 100 a jihar Yobe, don bunkasa sana’o’insu.

Da ya ke jawabi a madadin madugun na kungiyar ta Kwankwasiyya, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Suraja Kwankwaso, ya tabbatar da cewa wannan tallafi na daga cikin kokarin Dr Kwankwaso wajen rage talauci a tsakankanin al’umma mata da maza.

Wakilin na Kwankwaso ya kara da cewar, sun ware mata 100 da za su amfana da wannan tallafi na kara jarin Naira dubu10 ga kowanne daga cikin matan da za su amfana don kara habaka sana’o’insu na tuyar kosai, karago ko kunu, dan wake, dinki da makamantansu.

Ya ci gaba da cewar, sun zabi adadin matan da za su amfana da wannan tallafi ne a kusan kowacce daga kananan hukumomin Jihar 17 inda suka kasa su ya zuwa shiyya uku na majalisar dattawa.

Alhaji Siraja Kwankwaso ya kara da cewar, a yanzu haka wannan kungiya ta su ta kwankwasiyya karkashin daukar nauyin jagoransu Sanata Rabiu Musa kwankwaso sun bada irim wannan tallafi ga wasu matasa mata da maza fiye da dubu 8500, kuma nan gaba kadan suna da shirin kara bada wannan tallafi na karin jari ga mata kusan dubu 5 a Jihar Kano.

Shi ma Malam Nuiu Sarina daya daga tawagar ta kwankwasiyya shawartar matan ya yi da su ririta dan cin da suka samu don amfanin kan su da na iyalinsu.

Daya daga cikin matan da suka amfana da wannan tallafi na dubu goma-goma a madadin dukanin matan Amina Sarkin Hausawa daga karamar hukumar Fika godiya ga kungiyar ta kwankwasiyya dangane da wannan tallafi da aka ba su, kana ta kuma ja kunnen ‘yan uwanta mata da su kula da wannan jari da aka basu don na gaba su amfana.

 


Advertisement
Click to comment

labarai