Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Gano Sandar Majalisa Da Ta Bace

Published

on


Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta gano sandar Majalisan Dattawa da wasu ‘yan banga su biyar suka sace a Majalisar a ranar Laraba.

Mataimakin Kakakin rundunar, SP Aremu Adeniran, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya bayar jiya da safe, inda ya ce, sandar da aka sacen an yar da ita ne a karkashin gada a wajen garin kofar shigowa Abuja.

Da aka tuntube shi a jiyan kan jita-jitar cewa an kama ‘yan bangan da suka sace sandar, Adeniran, ya musanta cewa su ba su kama kowa ba.

Tun da farko a cikin sanarwar, Adeniran, ya ce, Shugaban ‘Yan Sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya dauki matakin gaggawa ta hanyar umurtan sashen binciken rundunar na musamman da ya dauki matakin tabbatar da gano sandar da aka sace.

Ya ce, Shugaban ‘Yan Sandan ya umurci da kulle dukkanin kofofin shiga da fita garin na Abuja domin bincike da nufin gano barayin da kuma sandar da aka sace.

Ya ce, ‘Yan Sanda sun shiga fafutuka da kuma tsattsauran bincike a dukkanin wuraren da ake kyautata zaton zauna gari banza na zama, wanda tsananta binciken ne ya tilasta wa barayin sanda yin jifa da ita su gudu.

Ya ce, an ajiye sandar ne a wani waje da ke karkashin gadar sama ta shiga garin na Abuja, inda wani mutumin kirki ya tsinkaye ta ya kuma shaidawa ‘Yan Sandan.

Ya kara da cewa, a yanzun haka sun tsananta binciken ganin sun kamo wadanda suka aikata wannan laifin domin su fuskanci shari’a.

Ya ce, rundunar ta yaba da hadin kan da al’umma suka ba ta, musamman masu motocin da ke bin sassan na Abuja, bisa hadin kan da suka ba su.

Ya kuma kara bayar da tabbacin cewa, rundunar ‘yan sandan a shirye take da ta bai wa al’umman babban birnin dukkanin tsaron da ya kamata, ta kuma tabbatar da zaman lafiya domin ci gaban Dimokuradiyya.

Majiyarmu ta jiwo tambayoyin da al’umma ke ta yi, kan yadda barayin har suka samu daman shiga har farfajiyar Majalisar suka kuma yi awon gaba da sandar ba tare da an kama su ba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai