Connect with us

LABARAI

 Osinbajo Ya Bukaci A Kyale Matasa Su Yi Takara

Published

on


Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayar da shawarar a kyale matasa su yi takaran mukaman siyasa a kasarnan. Ya fadi hakan ne domin a cewarsa, matasan ne suke da cancanta da kuma masaniyan fasahan zamani, ilimi da kuma sauran sassan tattalin arziki.

A cewar Osinbajo, idan har matasan Nijeriya sun kai munzalin da za su yi za~e, to ai kuwa sun kai munzalin da za su iya rike mukaman siyasa.

Mataimakin Shugaban kasan ya fadi hakan ne jiya a fadar shugaban kasa, sa’ilin da yake maraba da wakilan wata kungiya mai fafutukar ganin an dama da matasa a harkar siyasar kasarnan mai suna, ‘Not-Too-Young-To-Run campaigners.’

Kungiyar ta, ‘Not-Too-Young-To-Run campaigners,’ ta gabatar da wata bukata na ta ga Majalisar kasa, ta neman yin gyara a tsarin mulkin 1999, domin a rage shekarun tsayawa takara a kasar nan.

Mataimakin Shugaban kasan ya ce, ai cancanta ne abin dubawa wajen yin takara ba yawan shekaru ba.

Sai dai, ya shawarci matasan da su lakanci dukkanin cancantar da ya kamata, wanda hakan zai ba su damar yin shugabanci mai kyau.

Jagoran tawagar kuma babban daraktan kungiyar matasan mai suna, ‘Youth Initiatibe for Adbocacy, Growth and Adbancement (YIAGA) Africa, Samson Itodo,’ ya gode wa mataimakin shugaban kasan kan kasancewarsa tare da matasan na kasarnan.

Ya kuma tabbatar da cewa, tabbas mataimakin shugaban kasan ya yi amanna da kwarewa da kuma cancantar matasan Nijeriya a sassa daban-daban na tattalin arziki.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai