Connect with us

LABARAI

Bankin Jai’z Ya Kaddamar Da Makarantar Horos Da Ma’aikata A Zariya

Published

on


Ranar juma’a da ta gabata ne Bankin ja’iz ya kaddamar da Makarantar horos da ma’aikata a yankin bankin jaiz da ke Samaru Zariya

Babban manajan Daraktan Ja’iz na kasa Alhaji Hassan Usman ya sanar da haka cikin zantawarsa da manema labarai bayan an kaddamar da makarantar a Samaru Zariya

Hassan Usman wanda mukaddashin daraktan bankin ja’iz ,Alhaji Mahe Abubakar Mohammed ya wakilta,yace zuwa yanzu bankin yana da ofisoshi sama da talatin a fadin kasar nan.

Yakara da cewa suna da abokan harkar kasuwanci sama da dubu dari uku a fadin kasar na.

Mahe ya ce bankin ja;iz ya kasance na farko a wajen hurda kasuwanci ba tare da ruwa ba a fadin kasar nan.

 

Alhaji mahe ya baiyana cewa wannan makarantar zata rinka bada  horo na Sanin makamar aiki tare da horar da maaikata kan harkar kasuwanci na bankin a fadin kasar nam

Ya yi kira ga masu Hulda kasuwanci da Bankin Ja’iz a ko’ina a fadin kasarnam da suci gaba da hulda dasu , tare da basu alwashin biyan bukatunsu ba tare da shakku ba

A na ta jawabin ,Daraktan mai kula da bangaren horo maaikata Hajiya Hadiza I Bala race makarantar zata fara bada horo ga maaikatan bankin har su kimanin mutun Talatin na tsawan wata biyu

Ta ce wannan makarantar za ta ba da horo ga maaikata kan sanin makamar aiki da kwarewa a kan harkar aiikin banki


Advertisement
Click to comment

labarai