Connect with us

HANTSI

Shawarwari Ga Samari Masu Bukatar Aure

Published

on


Aure babban ni’ima ne a rayuwa. Aure alama ce ta cikar Dan Adam. Aure shi ne silar yaduwar al’umma. Sannan uwa uba Sunnar Ma’aiki (SAW). Ina samari masu neman aure? Ga shawarwari gare ku:

Da farko dai kafin ka fara neman aure, kamata yayi ka sami natsuwa kuma ka nemi yarinyar kirki, ko a cikin ‘yammata nagari ka nisanci guda 3, su ne kamar haka:

(1). Tagari ce amma ba ta sonka

(2). Uwarta ba ta da tarbiyar muslunci ko kadan

(3) Uwar ita ma ta gari ce amma tana nuna maka matsananciyar adawa

Sannan idan ka tashi neman aure ka sani cewa, ko motar da take karfe wacce za ka rika hawa ta kai ka duk inda ka keso a lokacin da kake so, dole sai ka samo lafiyayyiya sannan ka koyi yadda ake sarrafa ta, da yadda za ka lallaba ta har ta jima maka sosai. Dole ka rika kula da ita wajen kwalliyarta da gyaran injinta lokaci zuwa lokaci gwargwadon yadda wanda yayi ta ya tsara, kana wanke ta kuma kana ba ta irin man da take sha wanda zai gyara injinta. Kuma in ka tashi yin tafiya ba ka kure maleji ba, bare ta makale maka a cikin daji ko ta saka ka yi hatsari da sauransu.

To haka mace take, idan ka aura kai ma dole ka mike da yin wasu hidimomi matukar kana da bukatar ganin lafiyarta da kwanciyar hankalinka, da zama mai dorewa. Mace za ta rika yi maka hidima, amma kai ma maigida na kwarai akwai naka irin hidimar.

Shin ka auro wacce take sonka ?

Idan hark a yi dace ka auri mata tana sonka komai ka ke so za ka samu. Sannan ka zabo mai tarbiyya mai sanin addini da kama kai, mai kunya, bayan haka sai ka fara dora ta a kan hanyar da kai kake bukata, ta tafi a kanta.

Amma ka fahimci abu guda daya. Mace har kullum tana hukunci da zuciyarta ne, tana da tausayi da soyayya da daukan abu mai hatsari a matsayin karamin abu. Duk lokacin da zuciyarta ta baci za ta iya yin komai ba tare da tunanin abin da zai kai ya komo ba. Saboda dogaron da ta yi a kan zuciyarta, shi ya sa komai ilimin mace idan ranta ya baci ko kuma aka yi mata auren dole za ta iya yin komi. Kenan idan ka auri wace ba ta sonka don Allah ka yi mata uzuri. Ka yi kokari kaunarka ta shiga zuciyarta sannan ka nemi hakkokinka.

Maigida na kwarai muna yi maka zaton aiki da kwakwalwa sama da zuciyarka, kana da karancin nuna soyayya, da tausayi, ba kamar matarka ba, to amma kwakwalwarka takan nuna maka me ya dace ka yi?

Miji na kwarai ne wanda ya san darajar mace, yake ba ta hakokinta, idan mace ta yi aiki da zuciyarta to lallai shi kuma sai ya yi aiki da kwakwalwarsa. Amma ya dauki mace kamar abin hawa kullum sai dai ya yi amfani da ita ba wani kulawa da ita, gaskiya akwai matsala.

Yanzu ya za a yi ka zama maigida na kwarai bayan ba ka kulawa da matarka?

Ka nemi taimakon Allah (SWT) wajan samun mace ta kwarai, mai saukin kai wacce zata tafi dai-dai da bukatarka, sannan ka nemi wacce take son ka, ka zabo mai addini mai son muslunci, ka auro ‘yar namiji ba ‘yar mace ba. Sauran kuma ka baiwa Allah (SWT) ikonsa. Bayan nan ka shirya cewa zaka rika ganin abubuwan da baka so, amma haka Allah yayi ta dole sai kayi hakuri. karka taba saukowa dai-dai da matsayinta, sai gidanka ya lalace. kullum ka rika cewa ita mace ce kai kuwa namijine to sai a zauna lafiya.

 

Allah (SWT) ya bamu mata nagari, suma matan Allah ya basu maza nagari. Amin.


Advertisement
Click to comment

labarai