Connect with us

LABARAI

PDP Na Shirin Yin Maja Da Sauran Jam’iyyu?

Published

on


Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Abuja

Shugaban babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya ta PDP, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa jam’iyyar tana tattaunawa da sauran jam’iyyun adawa, da kungiyoyi masu zaman kansu, da tsofaffin shugabanni na kasa gabannin zaben 2019.

Da yake jawabi a lokacin taron gaggawa na kwamitin gudanarwar jam’iyyar a Abuja jiya Alhamis, shugaban na PDP ya ce makasudin fadada tuntubar tasu shi ne hada karfi da karfe domin kafa sabuwar gwamnati a 2019 don “ceto Nijeriya”.

Sai dai kuma shugaban bai yi cikakken bayani kan jam’iyyar maja take son yi da sauran jam’iyyu ba, illa kafe kai da fata da ya yi cewa dole ne su kori APC daga karagar mulki saboda ta gaza biya wa ‘Yan Nijeriya bukatunsu.

“Wannan mummunan koma-bayan da kasar ta fada ciki babban kalubale ne a gare mu a matsayin babbar jam’iyyar adawa mu sauya salon cimma burinmu tare da kwace goruba a hannun kuturu.

“Tuntubar da muke yi ta kai mu ga haduwa da sauran kungiyoyin da tamu ta zo daya da su, kuma ina tabbatar muku da cewa ana samun nasara.

 

“Nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, za mu samu wata hadakar siyasa mai karfi da za ta yi aiki tukuru domin ceto dimokuradiyya da kuma kasarmu daga hannun APC”.

 

Saboda haka, Secondus ya ce suna gayyatar kowa da kowa maza da mata su shiga cikin sahunsu domin tsamo kasar daga kangin rayuwa, matsalar tattalin arziki da kuma sha’anin tsaro.

Shugaban na PDP ya kuma ce abin da ya faru a Majalisar Dattawa na sace sandar mulki cin amana ne ga dimokuradiyya kuma ba wai kawai a yi tir da shi ba, ya kamata wadanda aka kama da laifi su dandana kudarsu a gaban shari’a bisa tanadin doka.

Gwamnoni da sauran jigajigan jam’iyyar duk sun halarci taron.


Advertisement
Click to comment

labarai