Connect with us

LABARAI

Kwamitin Kiyon Lafiya Na Kebbi Ya Ziyarci Fadar Sarkin Kabin Argungu

Published

on


Daga : Umar Faruk, Birnin-kebbi

Kwamitin kiwon lafiya a ma’aikatar lafiya ta Jihar Kebbi ya kai ziyarar wayar da kai  a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Samaila Muhammadu Mera a jiya a Argungu bisa ga shirin nan na asusun kiyon lafiya da gwamnatin Jihar Kebbi ke kokarin kafawa a jihar.

Kwamitin shirin  na asusun kiyon lafiya na jihar da ya kai ziyarar a fadar ya hada da Alhaji Muhammad Nasiru Gwandu a matsayin jagoran tawagar da ta kai ziyarar, wanda sauran mambobbin sun hada da Mustapha Tata Argungu, Shehu Muhammad daga hukumar WHO,  Alhaji Hassan Ibrahim MaiGundi da kuma Muhammad Nasiru Dakingari dukkansu a cikin Kwamitin na wayar da kan jama’a kan muhimmancin shirin asusun kiyon lafiya da gwamnatin jihar ta kebbi ke son bulowa dashi kamar yadda dokar tsarin asusun kiyon lafiya na kasa ya bayar da dama ga kowace jihar a kasar nan na iya yin nata tsarin asusun kiyon lafiya wanda zai iya yin dai dai da jama’arta.

 

Hakazalika, Muhammad Nasiru Dakingari ya bayyana wa masarautar cewa “wannan tsarin saboda ne shi ya sa aka fara taron masu ruwa da tsaki kan harkar asusun kiyon lafiya a jihar ta kebbi domin tattaunawa kan sabon tsarin da ake son a fito dashi ga jama’ar jihar ta kebbi”.

Yace mun kawo ziyara ne a wannan masarauta mai albarka domin ta basu nata shawarwari kan tsarin da akeso a yima wannan sabon shirin domin samar da sauki ga jama’armu  a lakacin da duk wata matsala ta asibiti tataso ga mutanenmu.

Har ilayau ya nemi masarauta da kuma sarkunan muna gargajiya da su taimaka da kuma bada goyun bayansu ga wannan shirin da  gwamnatin Jihar Kebbi ta fito dashi domin amfani jama’armu.  Ya ce yanzu ne ake so a tatara bayanai da kuma shawarwari domin mayar da su doka wadda za ta tabbatar da tsayuwar shirin a cikin jihar ta kebbi.

Duk masu ruwa da tsaki a harakar kiyon lafiya an sanya su a cikin wannan shirin saboda haka ya yi amfani da wannan dama ta ziyarar fadakarwa kan yadda shirin asusun kiyon lafiya na Jihar Kebbi za ya kasance domin gaya wa sarkin Kabin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad mera cewa sarakuna na cikin tsarin wannan shirin domin shirin yana tafiya ne daidai tsarin Shari’ar musulumci.

Daga karshe ya kuma amsa tambayoyin da Sarkin Kabin Argungu ya yi domin kara sanin yadda tsarin shirin asusun kiyon lafiya na Jihar Kebbi zaya kasance da kuma wasu tambayoyi da ubannin kasar yankunan masarautar Argungu su kayi.

Shi ma da yake jawabain ga Kwamitin asusun kiyon lafiya na Jihar Kebbi da suka kaimasa ziyara a fadarsa da ke Argungu a jiya yace “ zamu tabbatar da shirin ya samu nasara a jihar ta mu”. Ya kuma bada shawarar cewa a tabbatar da mutanen da zasu jagoranci wannan shirin mutane ne nagari kuma masu mutunci ga jama’arsu.

Daga nan ya umurci ubannin kasar yankin masarautarsa da su wayarwa jama’arsu da Kai kan wannan sabon shiri da gwamnatin Jihar Kebbi ta fito dashi domin samar wa jama’armu sauki wurin kiyon lafiya a cikin jihar mu ta kebbi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai