Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Halasta Wa EFCC Hana Fayose Amfani Da Asusunsa Na Banki

Published

on


 Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Abuja

Wata Kotun Daukaka Kara a birnin Ado-Ekiti da ke Jihar Ekiti ta baiwa Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arzikin Kasa da Zambar Kudi (EFCC) damar hana Gwamna Ayo Fayose amfani da asusunsa na banki.

Maishari’a J.S. Ikeyegha, wanda ya karanta hukuncin da alkalan kotun su uku suka yanke, ya umurci a hana Gwamnan amfani da asusun ajiyarsa na Bankin Zenith.

Idan ba a manta ba dai, a watan Disambar 2016, Maishari’a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Ado-Ekiti ya umurci EFCC ta dage hana Gwamnan amfani da asusun, bisa binciken da ta ce tana yi a kan wasu kudaden da take zargin na kamuya-muya ne da aka zuba a ciki

Sai dai da yake EFCC ba ta gamsu da hukuncin ba, sai ta garzaya kotun daukaka kara domin sake bin kadin lamarin. EFCC ta ce umurnin ya ci karo da wanda Maishari’a M.B Idris ya bayar a Legas, wanda ya halasta ma ta hana Gwamnan amfani da asusun har sai an kammala bincike.

Ko ya za ta kaya a tsakanin Gwamnan da EFCC? Lokaci ne kadai zai nuna.


Advertisement
Click to comment

labarai