Connect with us

LABARAI

Kafa Asusun Tallafa Wa Dalibai Daya Ne Daga Manyan Ayyukanmu –Sanata Kani

Published

on


Daga  Abba  Ibrahim Wada Gwale

Shugaban kungiyar dalibai ta jami’ar Bayero da ke kano, Muhammad Sanusi Kani, ya bayyana cewa kafa asusun tallafa wa dalibai marasa karfi da gwamnatinsa ta yi yana daya daga cikin ayyukan da ta ke alfahari da su.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke sabuwar jami’ar inda ya ce akwai tsare-tsare da gwamnatinsa ta zo da su kuma a hankali za su cigaba da aiwatar da su domin cigaban daliban makarantar.

Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa tana iya kokarinta wajen tabbatar da ganin cewa ta sauke nauyin da aka dora mata da kuma cika alkawuran da suka dauka a yayin yakin neman zabe.

Ya kara da cewa duk da cewa akwai matsaloli da gwamnatinsa take fuskanta amma hakan baisa sunyi kasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da ganin komai yana tafiya yadda ya kamata a gwamnatin.

Kani, yace wasu daga cikin ayyukan da gwamnatinsa takeyi sanatoci da masu ruwa da tsaki acikin gwamnatinne suke yi da kudadensu domin dai a tabbatar an sauke nauyin da yake kansu sannan kuma ya yi kira ga masu yiwa gwamnatinsa zagon kasa da su yi adawa irin wadda ya kamata batare da suna yin abinda zai dinga tauyewa dalibai hakkunansu ba.

“Inason in ja hankalin dalibai cewa akwai wasu mutane da suke musu bita da kulli a gwamnatinsu domin su samu matsala saboda haka bazasu saki jika ba kuma zasu cigaba da ayyuka domin cigaban dalibai”. In ji Sanata Kani.

A karshe ya bayyana wasu daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatinsa tasamu nasara akai sun hada da rokon hukumar makaranta akan kada ta karawa dalibai kudin makaranta sannan kuma an samu ragin kudin makarantar a wasu tsangayun na jami’ar.

Yace har ila yau gwamnatinsa tayi kokarin samar da injin transifoma ga mutanen unguwar dan bare sakamakon akwai dalibai dayawa da suke zaune a unguwar sannan kuma sunyi kokarin gyara kujerun karatu da suka lalace a dakunan karatu na jami’ar.

Sannan kuma gwamnatinsa ta yi kokarin bijiro da wani tsari na tallafawa dalibai yan asalin jihar nan inda dalibai 200 ne sukaji gajiyar shirin a wannan shekarar sannan kuma shekara mai zuwa ma adadin daliban zai iya karuwa.

Ya kuma godewa hukumar jami’ar Bayero bias goyon baya da suke bawa gwamnatinsa sannan ya jinjinawa dalibai suma bisa kokarinsu na ganin komai yatafi yadda aka tsara.


Advertisement
Click to comment

labarai