Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Ja Kunnen Masu Zuwa Aiki A Makare

Published

on


Shugaban ma’aikatan jihar Bauchi, Alhaji Liman Bello ya gargadi dukkanin wani ma’aikacin gwamnati da ke sakaci da aikinsa ko kuma masu kin zuwa aiki a kan lokaci ko kuma masu tashi daga wajen aikinsu gabanin lokacin tashi a wajen aiki na zahiri da cewar za su dandani kudarsu a hanun gwamnatin.

Shugaban ma’aikatan ya yi gargadin ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata zuwa wasu manyan ma’aikatun jihar Bauchi a Larabar nan, domin gane wa idonsa yadda aikin gwamnatin ke tafiya da kuma duba halin da ma’aikata suke ciki domin yin gyara a inda ake da bukata.

Liman ya bayyana cewar dukkanin ma’aikacin da bai zuwa bakin aiki ko kuma wanda ke tafi a ba a lokacin tashi ba ko kasu zuwa a makare da cewar suna cin haram, ya nemi ma’aikata da su kasance masu tsarkake albashinsu domin cin halaliyarsu.

Alhaji Liman Bello da shi da ‘yan takagarsa sun isa ma’aikatan muhalli da safiyo ne da misalin karfe 8.30 na safiya, inda suka samu tarba daga Daraktan kula da sashin mulki na ma’aikatar  Alhaji Abdulhamid Mohammed.

HOS ya kira yi ma’aikatan da suke aiki a wannan ma’aikatar da su tabbatar da bin dokoki da ka’idojin aiki domin kauce wa fuskantar fushin gwamnati mai ci.

Haka kuma tawagar ta Liman Bello ta isa zuwa ofishin shiyya na hukumar ilimi da karfe 8:55 na safe, hukumar da ke kula da asibitoci na jihar da misalin karfe 9:20nf, haka kuma ya isa ma’aikatar wuta, fasaha da kuma kimiyya da misalin 9:30nf, inda ya jinjina wa babban sakataren hukumar da ke kula da asibitoci na jihar Bauchi Dakta Abdulazeez Manga a bisa kokarinsa na tabbatar da jin dadi da walwalar ma’aikatansa gami da tabbatar da suna gudanar da aiyukansu yadda ya dace domin daukaka sha’anin lafiya musamman kan kokarinsa wa manyan asibitocin jihar.

Da yake ganawa da manema labaru bayan kammala ziyarar, shugaban ma’aikatan, Alhaji Liman Bello ya bukaci dukkanin ma’aikatan jihar da su sauya halayensu na rashin zuwa aiki kan lokaci ko kuma barin wajajen aikinsu gabanin lokacin da aka dauke su aiki don yi a wajen aiki, ya kuma bayyana cewar bai kamata ma’aikata suke shigo da wasu dabi’u cikin aiki ba, ya bukacesu da su yi amfani da ma’aikatunsu domin daukan aiki zuwa ga babban mataki don yi wa jama’an jihar hidima.

Bello ya kuma fa ce gwamnatin ba za ta zura ido tana kallon wasu na sakaci da aiyukansu ba, don haka ne ya bayyana cewar dukkanin wani ma’aikacin da bai bin dokoki da kuma ka’idon aikin gwamnati zai fuskacin fushinsu.

Ya turanar da ‘yan uwansa ma’aikata kan irin kokarin da gwamnatin jihar ta ke yi wa ma’aikata musamman wajen biyansu albashinsu a kan kari gami da tabbatar da cewar suna samun yanayin aiki mai nagarta kuma yadda ya dace don haka ne ya nemi su kansu ma’aikatan da su ma a tasu fannin su sanya kokarinsu don a samu kyautata aiki.

Ya kuma sha alwashin cewar zai ci gaba da sanya dukkanin abun da ya dace wajen dakile dabi’ar nan ta rashin zuwa aiki ko kuma latti a a wajen aiki, ya bayyana cewar dukkanin ma’aikacin da ke sakaci da zuwa wajen aiki ya sani bai cin halaliyarsa, ya nemi kowani ma’aikaci ya ke tsaftace albashinsa ta hanyar yin aiyukan da gwamnati take tsammani daga garesa domin yi wa jama’an jihar hidima tukuru.

Daga karshe ya bayyana cewar gwamnatin jihar mai ci a wannan lokacin za ta ci gaba da tabbatar da cewar kowani ma’aikacinta na samu yanayin aiki yadda ya dace domin kai jihar mataki na gaba kuma cikin nagarta.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai