Connect with us

LABARAI

2019: Buhari Ya Cancanci Sake Tsaya Wa Takara –Sani Fema

Published

on


Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Tsohon shugaban hukumar wasanni na jihar Yobe, Alhaji Muhammad Sani Fema, ya bayyana cewar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cancanta da sake tsayawa takara a karo na biyu, don cigaba da gyara irin barnar da gwamnatin PDP ta yi a tsawon shekaru 16 da suka yi suna mulkar kasar nan.

Alhaji Sani Fema ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilinmu a garin Damaturu bisa ga bayyana sake tsayawarsa takara a zaben da ke tafe na 2019 da shugaban kasar ya sanar a kwanakin baya wanda hakan ya kawo karshen cece-kucen da ake ta yi dangane da yiwuwa ko rashin yiwuwar sake tsayawar shugaban.

Kamar yadda ya ce tabbatacce ne cewar, Shugaba Buhari ya yi matukar taka rawar gani a fannoni da dama musamman bisa alkawuran da ya dauka ya yin yakin neman zabe a 2015 kan abin da ya shafi kawo karshen take-taken masu ta da kayar bayan Boko Haram da magance mummunar dabi’ar nan ta cin hanci da rashawa da a baya ke kokarin lakume kasar nan, da kuma habaka tattalin arzikin kasar nan. Alhaji Sani Fema ya ci gaba da cewa duk wanda zai auna irin ayyukan da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ta aiwatar a ‘yan shekaru 3 kacal da ta yi akan mulki musamman kan abin da ya shafi harkokin tsaro, da tattalin arziki, da yaki da almundahana na kwasar dukiyoyin jama’a, lallai za a ga cewar ya zarta mulkin PDP na shekaru 16 inganci.

Ya kara da cewa in aka dora wannan gwamnati a mizani na hakika sai a  ga cewa, gwamnatin a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta cimma muhimman nasarori musamman wajen ayyukan raya kasa da suka hada da gina hanyoyi, samar da aikin yi ga matasa, da inganta tattalin arziki, da kara inganta harkokin ilimi, samar da tsaro ba tare tsumbure da makamantansu  ba, fiye da kashi 75 cikin 100.

Don haka ya kirayi dukanin al’ummomin Jihar Yobe da na Jihohin Arewa maso gabas da na dukanin kasa baki daya da su goya baya ga wannan mataki na shugaban kasa na sake tsayawa takara a karo na biyu don ci gaba da kudirinsa na ceto kasar nan da al’ummominta daga halin ni ‘ya su.


Advertisement
Click to comment

labarai