Connect with us

LABARAI

Za Mu Dauki Matakin Hukunta Wadanda Suka Jefi Gwamna A Sansanin Gudun Hijira –Kwamishinan Yan Sanda

Published

on


Daga Zubairu T. M. Lawal , Lafia

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Nasarawa Ahmad Bello ya ce, ya zuwa lokacin zantawa da manema labarai ba su kama kowa ba amma nan bada dade wa ba za su zakulo wadanda sukayi wanan aika aikan a hukunta su.

Kwamishinan ya ce; wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba a cikin yan gudun hijira suke ba sun dai shiga rigar yan gudun hijirar ne suke aikata danyen aiki.

Ya kara da cewa ; yan gudun hijira iyakar yadda suke shi ne filin makaranta amma wadanda suka zo suka tsare hanya suna jifa da dutse ba yan gudun hijira bane.

Wanan dalili ne ya sanya ‘yan sanda suka dauki matakin korarsu ta hanyar yin amfani da barkonon tsohuwa saboda doka ce ta ce duk wanda ya tare hanyar Gwamnati to ko waye Jami’an tsaro sun hukunta shi.

Ya ce, “hakkin Jami’an tsaro ne su kare Gwamna saboda hakin kulawanshi yana karkashin su. Gwaman ya je wannan wuri ne da nufin duba yan gudun hijira lokacin da Gwamana ya fara jawabi sai muka ga hayaniya yayi yawa shiyasa mukabada umurnin abar gurin saboda sha’anin tsaro.”

Kwamishinan ya kara da cewa, wasu na ganin cewa lokacin da ake kashe-kashen Jami’an tsaro ba su je wurin ba ya ce, “Ai mu ba Allal musuru gare mu ba idan abu ya faru sai an sanar damu muke sani idan aka sanar damu sai mu shirya gamayyara Jami’an tsaro da zamu tura domin kawo saukin lamarin.”

Amma abin da ba a sanar da kai ba a ce ba ka je ba ta ya ya za ka sani idan ba a sanar maka ba.

Gwaman Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura ya janye ziyarar ta shi ta zuwa sansanin yan gudun hijirar dake garin Keana da Obi dama Awe.


Advertisement
Click to comment

labarai