Connect with us

LABARAI

’Yan Sara Suka Sun Rautanata Mutane Biyar A Kusa Da Cibiyar ‘Yan Jaridu Ta Bauchi

Published

on


Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Wasu matasa ‘yan sara suka sun kai hari cibiyar sadarwa da kasuwanci ta Reinsurance House da ke kan titin Ahmadu Bello da ke Bauchi inda suka raunana mutane da dama yawancin su mawaka da kuma wadanda ke halartar cibiyar don gudanar da bincike kan sadarwa irin ta zamani da bukukuwa bayan haka  kuma sun lalata dukiya mai yawa a yayin wannan farmaki.

Harin an kai shi a wannan larabar da rana inda yawanci suka fi aiwatar da ta’addancin su inda suka fi illata mutane shi ne ofishin Shamaki Media wata cibiyar sadarwa mai tallace tallace da wayar da kan jama’a, wacce ake ganin bata ga maciji da juna da  gwamnatin Jihar Bauchi saboda yawancin tallace tallacen adawa da ake yi don watsawa ta kafafen labarai su ke gudanar da shi.

Cikin mutanen da suka raunata mafi tsanani akwai Haruna Aliyu  NIngi da Ali Shamaki da Jibrin Abubakar da Naziru Danautan mawaka da kuma wasu mutane da dama da tsautsayi ya fada kan su a daidai lokacin da suka halarci cibiyar don gudanar da ayyukan su na yau da kullum kamar yadda suka saba. Al’amarin ya zamo abin takaici saboda ganin maharani rana tsaka suka je a kan baburan hawa masu dauke da mutane uku uku dauke da makamai inda shigar su ke da wuya suka fara saran mutane, yadda wasu da dama kafin saran ya je kan su suka rika fadowa daga kan beni mai hawa biyu suna karyewa.

Yayin das hi kuma Aliyu Shamaki wanda ke yawan tallar sukan gwamnatin M. A. Abubakar aka raunata shi a hannu da wasu sassa na jikinsa da wuka, shima Haruna Aliyu Ningi mai wakar PDP shima ya samu rauni sosai, lamarin da ya sa mutane a halin yanzu suka kara razana da lamarin na mata ‘yan sara suka a garin Bauchi.

Matsalar sara suka a Jihar Bauchi an jima ana fama da ita amma jami’an tsaro da sarakuna da iyayen yara suka kokarta wajen shawo kan matsalar,  amma zuwa wannan lokaci lamarin ya fara dawowa inda matasan da ake ganin wasu na samun daurin gindin wasu ‘yan siyasa ko kuma masu aikata laifuka a boye suka fara dawo da wannan mummunar dabi’a.

Bayan aukuwar lamarin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta tura jami’anta amma basu samu nasarar kama ko mutum guda ba saboda duk sun hau mashinan da suka zo da su sun gudu. Amma kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan ta’adda.

Kuma ya shawarci jama’a da su rika ba ‘yan sanda bayanai game da masu aikata laifuka don a samu damar magance irin wannan matsala.


Advertisement
Click to comment

labarai