Connect with us

LABARAI

Ya Kamata A Kafa Kwamitin Taimakekeniya A Jihar Kano

Published

on


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An shawarci al’umma a unguwannin jihar Kano su kafa kwamitoci na taimakekeniya a tsakaninsu musamman ma ta tallafawa masu matsaloli a harkar lafiya ,ilimi da ciyarwa wannan shawara ta fitone ta bakin Alhaji Ali Nuhu Wali da yake zantawa da wakilimmu.

Ya ce yanada matukar muhimmanci ace kowace unguwa su yi kwamiti dazai hada da dattawa wadanda za su rika tuntubar masu hannu da shuni da sauran al’umma dansu rika taimakawa bukatun al’ummarsu.

Ali Nuhu Wali ya ce kullum ka bude rediyo sai kayi tajin neman taimako wani na Asibiti ko makaranta wani harkar rayuwa,wanda sai mutane sun taru sun kawo canji da kansu kamar yanda Allah ya ce baya canzawa sai mutane sun hadu canza,wannan zai taimaka wajen kulada tsaro ta unguwa da za’a rika kulada masu aikin tsaro da hakan zai rage sace-sace da sauran miyagun dabi’oi.

Ya ce wannan gidauniya idan kowace unguwa ta dauka asa iyayen kasa a ciki tun daga kan hakimai dagatai da masu unguwanni da jami’an tsaro na yankin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro wannan zai kawo raguwa aikata laifuka domin harkar laifi abune mai zaman kansa yanada mataimaka da zakaga in an toshe wannan laifin sai wannan ya bullo,dole sai an hadu gaba daya an taimakawa jami’an tsaro yakamata kowace unguwa tayi hobbasa sai a sami sauki.

Alhaji Ali Nuhu Wali ya ce kullum zakaji ana neman taimako,da anyi Gidauniyar Kano wanda ba’a maganarta yanzu.Yakamata yanzu a kafa Gidauniya a kowace unguwa da mutane za su hadu su hada kudi dan anfanawa kansu ta danka tafayarda gidauniyar a hannun masu gaskiya da rikon amana da bibiyar yanda ake aiwatarda kudinda ake samu wannan zai taimakawa cigaban al’umma ta dogaro dakansu a bukatunsu ba tareda sun jira gwamnati ba ko kuma suna zuwa neman taimako ta kafafen labarai.

Ali Nuhu Wali yaja hankalin iyaye akan su rika kulawa da kyautata tarbiyar ya’yansu dan gina al’umma ta gari masu anfani a rayuwarsu


Advertisement
Click to comment

labarai