Connect with us

LABARAI

Sanya Ni Cikin Barayin Kasa, Bata Suna Ne –Secondus

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, ya ce, zargin da ake yi na cewa, yana cikin mutanan da suka handame dukiyar kasarnan kokarin bata suna ne kawai.

A cikin bayanin da mai ba shi shawara kan harkokin manema labarai, Ike Abonyi, ya sanya wa hannu, Mista Secondus, ya ce, duk wani kokarin bata suna da tursasawa daga abokan adawa na gwamnatin tarayya ba za su hana shi ci gaba da kokarin da yake yi na sake farfado da Jam’iyyar na shi ba.

“Ofishin hulda da manema labarai na Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya lura da yunkurin da gwamnatin tarayya da kuma Jam’iyyar ta ta APC ke yi na neman bata ma sa suna da wasu kagaggun bayanai da nufin taka masa burki a kokarinsa na sake dinke Jam’iyyar sa.”

Ofishin yada labaran na shi ya ce, “Mista Secondus, ba zai so tsayawa cacan baki da gwamnatin ba, kan lamarin da yake a gaban kotu, “Amma abin takaici sai ga shi, gwamnatin tana raina umurnin kotu tana kuma taka doka yadda ta ga dama, ta tsaya da neman bata suna a kafafen yada labarai, domin ta bata shaksiyar abokanin adawanta.”

Wannan gurguwar dubarar ta su ba ta yi nasara ba, domin kuwa ‘yan Nijeriya sun fahimci gurguwar dubarar ta gwamnatin da ke shirin balbalcewa.

“A yunkurin na su na neman ko ta wace hanya su bata masa suna, sun kasa ma daidaita alkalumman na su na karya, Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya kasa bayyana ranar da ya ce an karbi kudaden da yake kokarin yin kagen a kansu, sannan kuma ya kasa bayyana wa ya karbi kudin, Secondus ne ko kuma mutumin da babu shi ne da yake lakabawa suna, Chukwura, wanda ya ce bai san sunan uban shi ba.

“Tun a shekarar 2015 suke kokarin binciko sunan mahaifin mataimakin karyan da suke cewa wai na Secondus din, a wata ganawar sa da manema labarai ranar 29 ga watan Maris 2018, Lai Mohammed, cewa ya yi, Secondus, ya karbi kudaden ne ranar 19 ga watan Fabrairu 2015, su kuma hukumar EFCC, suka ce, an karbi kudin ne a ranar 9 ga watan Fabrairu 2015, a wani kaulin na hukumar ta EFCC, kuma cewa suka yi ranar 2 ga watan na Fabrairu ne aka karba.

Shugaban na PDP, ya bayyana takaicin sa, da hadarin da ke tattare da yadda hukumar ta EFCC, wacce ya kamata a ce tana yaki ne da masu neman kashe tattalin arzikin kasa, sai ga shi tana zama wata shirwan gwamnatin APC,  da ake amfani da ita wajen farautar ‘yan adawa.

Ya kuma kalubalanci gwamnatin ta APC da duk wata hukuma da ke da rahoton wata tabargaza ko satan da ya yi, da ta zo su gamu a kotu da cikakkun shaidun ta, ba a tsaya a kafafen yada labarai ba.

“Ba bukatar  yin magana cikin jaridu kan abin da yake gaban kotu. Idan gwamnati tana da wata magana, kamata ya yi su nufi kotu kawai.”

“Ni ban karbi kwabo daga hannun kowa ba. Ban kuma sanya wani ya karban mani kudi ba, ban kuma sanya hannu kan kowace takardar karban kudi ba. Kokarin bata suna ne kawai, ba kuma zai yi aiki ba.

“Ba wani bata sunan da za su yi wa mutane da zai sanya APC ta sake cin zabe, bayan mutane sun gano su sun kuma yi watsi da su, 2019 kawai muke jira.


Advertisement
Click to comment

labarai