Connect with us

LABARAI

Mun Yaba Da Kalaman IBB Kan Sanata Makarfi –Kungiyar Matasan Nijeriya

Published

on


Daga Abubakar Abba

Kungiyar matasa da suka fito daga yankin Kudu maso Kudu na kasar nan sun jinjinawa tsohon Shugaban kwamitin riko na kasa na jamiyyar PDP kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi saboda nuna ladabin sa da kuma jajircewar sa akan dorewar jamiyyar a kasar nan.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar wadda kuma Shugaban shiyyar Kudu maso Kudu Honarabil InioriboTamunotonye ya sanyawa hannu ya sarawa Sanata Makarfi sarawa Sanata Makarfi akan nuna wannan halin na dattako wajen yiwa jamiyyar biyayya.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ce, akan martanin da aka danganta cewar tsohon Shugaban kasa na mulkin soji Janar Ibrahim Babangida mai ritaya ya yi a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan Kwamitin zartarwa na jamiyyar PDP da Shugaban PDP na kasa Yarima Uche Secondus ya jagorance su zuwa gidan IBB dake garin Minna.

Tsohon Shugaban kasar a lokacin ziyarar, ya yaba da biyayyar da wasu jigogin PDP suka yi a lokacin ziyarar.

Sanarwar taci gaba da cewa,” mu waklilan kungiyar matasan da suka fito daga jihohi shida na Kudu maso Kudu muna maraba da yadda tsohon Shugaban kasar ya karbi jigogin jamiyyar PDP hannu bibiyu a lokacin ziyarar.

A cewar sanarwar, bayan yin fashin baki, mun yi amanar cewar, mai girma Sanata Ahmed Makarfi, tsohon Shugaban Kwamitin rikon kwarya na PDP shine yafi chanchanta ganin cewar shine jigo babba na PDP, wanda biyayyar sa ga PDP a shekaru da dama da suka shige bata misaltuwa.

Sanarwar ta kara da cewa, a yanayin siyasar Nijeriya irin ta yau, zai yi wuya a samu dan siyasa da yake ta yin biyayya ga PDP har da lokacin da take fuskantar kalubale kamar Sanata Makarfi.

Ta bayyana cewar, abin mamaki shine, duk da cewar Sanata Makarfi ya fadi a takarar kujerar Sanata a shekarar 2015 da kuma yadda tsohon Shugaban Kwamitin riko na PDP Sanata Ali Modu Sheriff, ya yamutsa

hazon siyasar cikin gida na PDP, amma Sanata Makarfi ko gizau bai nuna ba har sai da yaga PDP ta tsaya da kafarta.

A cewar sanarwar saboda nuna halin dattako da Sanata Makarfi ya yi, hakan ya baiwa dan takarar Kujerar Sanata a PDP Sanata Ademola Adeleke sukunin lashe lashe zaben.

Sanarwar ta ce, Sanata Makarfi ya tserewa tsara idan ana maganar yiwa PDP ladabi da kuma kasar nan, har da matakan gwamnati.

A cewar su, a matsayin mu na matasa, munyi amanra cewar, samun irin su Makarfi yana da wuyar gaske kuma ya kamata ayi koyi da irin wannan halayen nasa don yin aiki tare musamman don ya fito takarar shugabancin kasar don ya tsamota daga cikin mawuyacin halin data samu kanta.

A wani labarin kuma, kungiyar matasa da suka fito daga shiyyar Arewa Maso Yamma da suka hada da jihohin Kaduna da Katsina, Kano daSokoto da Kebbi da Zamfara, da kuma Jigawa suma sun gudanar da taro a jihar Kano, inda suma suka mayar da martani akan furucin da ake dangana shi da IBB akan matsyin na zabubbuka 2019.

A cewar kungiyar, kamar yadda IBB ya zayyana kyawawan halayyen shugaba na kwarai, hakan ya nuna a zahiri cewar, Sanata Makarfi shine kadai yake da irin wadannan kyawawan halayen, idan akayi la’akari da kujerar Gwamnan jihar Kaduna da ya rike har tsawon shekaru takwas musamman yadda ya yi kokarin samar da wadataccen tsaro ba kamar a wannan mulkin da ake yi ayau ba.

Kungiyar ta bayyana cewar, dukkan hukomomin da Makarfi ya kafa a lokacin yana gwamnan har yau ana cin gajiyar su a jihar musamman yada suka inganta fannin rayuwar ‘yan jihar tun daga fannin ilimin zamani da aikin noma da raya karkara da inganta tattalin arzikin jihar.

Sakamakon irin wadannan dimbin ayyukan, hakan ya sanya Makarfi ya shiga gaban sauran.Kungiyar ta kara da cewa, duk da cewar akwai sauran ‘yan takara da suka chanchanta tsayawa, amma idan ana maganar matashi, Makarfi ne ya dace da wannan damar.

Sanarwar ta kara da cewa, “ matsayin mu na ‘yayan kungiyar, muna son mu sanar da duniya cewar, duk da cewar IBB yana jin an barshi a baya, saboda wasu kurakurai da ya yi a baya, munga shugaba gwarzo kuma uba wanda kuma za’a yi koyi dashi wanda kuma yake dauke da halayen Marigayi Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, Dakata Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo da Olusegun Obasanjo harda shi IBB kamar Ahmed Mohammed Makarfi.

Bugu da kari, sanawar tace, duk da cewar a yankin Arewa maso Yamma muna da mutane kamar su Sule Lamido tsohon gwaman Jigawa da Shekarau tsohon gwamnan Kano, amma dukkan su, munyi amannar cewar, su marawa Makarfi baya da bashi dukkan goyon bayan da ya dace don tunkude APC daga kan mulki, musamman yadda ta jefa talakawan kasar nan a cikin kngin yunwa da fatara.

Wadanda suka hadu yayin sanarwar sun hada da Zainab Al-Amin. Ko’odineta, Arewa Maso Yamma da Kakinta, Stephen Bala Gora. Sai Ambasada Sunny Nnaemeka StClement, Ko’odineta, Kudu Maso Gabsa, da Nze Ugo-Akpe Onwuka Oyi of Oyi II), Ko’odineta na jihar Anambra.


Advertisement
Click to comment

labarai