Connect with us

KASUWANCI

Mene Ne Sirrin Tsawon Ran Masakar Funtuwa?

Published

on


Daga Hussaini Baba

A shekarun baya Masakun Funtuwa Testiles, Gusau Testiles da ta Kaduna Testiles, na da ga cikin manyan masakun da al’ummar Arewancin Kasar nan ke cin moriyar su kuma gwamnatocin ke alfaharin d su wajan samun kudin shiga.

Sai gashi yanzu haka Masakar Kaduna Testiles, ta samun shanyewar Rabin Jiki, wani sashe ne kadai nata ke aiki yanzu haka.

Wannan kuma ya sanya cewa ‘Dubannan Ma’aikata ne suka rasa ayyukan su sakamakon ciwon da ya samu Masakar.

Ita kuwa ta Gusau watau Gusau Testiles , ta yi doguwar suman da yasa duban nan ma’aikatanta an sallame su da ga aikin a cikin masakar wanda yanzu haka mutu kwakwai rai kwakwai.

Funtuwa Testiles kuwa yanzu haka tana cigaba da aiki kai kace ko ciwon kai ba ta taba yi ba, balle shanyewar rabin jiki ko kuma Doguwar suma.

Wannan ya sa LEADERSHIP A Yau ta yi bincike na musamman akan wane sirri ne ya sa wannan masakar ta yi tsawon rai, ta tsallake annubar, durkushewar masana’antun Kasar nan duk da matsalar wutar lantarki?

Waiwaye adon tafiya ita dai Masakar Funtuwa Testiles, yanzu haka ta kwashe tsawon shekaru arba’in tana aiki, babu dare babu rana har zuwa yau da nake wannan rubutu a kan ta.

Masakar Funtuwa Testiles ta fara aiki ne da ma’aikata ashirin kuma yanzu haka tana da ma’aikata na dum-dum dum, dubu daya da dari biyar sai kuma masu kwantaragi dari hudu da hamsin. kuma alokacin kaka ana daukar mata dari dan tsuce duwatsu da manona ke sa wa a cikin Audugar don algushu.

Wannan katafariyar Masakar da ma’aikatanta ke yi wa mata kirari da lahira; Lahirar Auduga don duk audugar da ta shiga cikin wannan masakar, zabi biyu ne gare ta ku ta kuma Zare ko Yadi.

’Ya’yanta ne kadai ke fita watau (Gurya) don da ita guryar ne ake irin don samun wacce za su shuka a shekara mai zuwa.

Haka kazalika kuma, Funtuwa Testile na Saka, yadiddika masu dauke da Auduga zalla wace ke raya fatar jikin dan adam.

Kuma ta samar da Yadi mai akoko, Farin yadi alawayyo da kuma yadin kuwa da kuwa watau wanda ake yin likkafani da shi da kuma wanda ake wa Sarakuna rawuna duk Funtuwa Tedtiles ne ke samar da su.

Wannan ya sa kamfanonin katifu daga ko’ina cikin kasar nan ke zuwa ana sarrafa masu yadiddikan da suke bukata, kalarsa da ingancinsa da kuma yawansa.

LEADERSHIP A Yau ta binciko sirrin tsawon ran wannan masaka ne na ganin ko da yaushe tana ware kudade na musamman don a yi wa kamfanin addu’o’i a masallatai da wurin ibadu. Sai kuma yin Yadiddika masu inganci wanda babu almundahana a cikinsa watau suna aiki tsakani da Allah babu almundahana a cikinsa.

Sai kuma babban sirrin shi ne biyan ma’aikata albashin su akan lokaci, tun kafin gumin jikinsu ya bushe ana biyansu albashi kuma sai Allah ya albarkaci ma’aikatan na masakar da sadaukarwa daga cikin albashinsu suna ba masallatai gudunmuwa da kuma yi wa kamfanin addu’oi don ganin bai durkushe ba. Kuma wannan masaka kasha tamanin da biyar masu cin gajiyarta ‘yan jihar Katsina ne musamman ma ‘yan yankin funtuwa.

Kuma Masakar ta samu lambobin yabo daga jama’a da gwamnatina taimaka wa wajen samar wa al’umma aikin yi.

Sai dai wani kalubalen da masakar ke gamuwa da shi shi ne na Algushin da wasu miyagun manoma ke yi na sanya ruwa a cikin Audugar su don ta kara nauyi wajen awo wasu kuma na sanya Duwatsu ko Yashi.

LEADERSHIP A Yau ta ji ta bakin tsohon ma’aikicin masakar wanda yayi ritaya da kashin kansa Malam Yusuf Auwal Funtuwa ya bayyana mata cewa, ‘lallai Masakar Funtuwa Tedtiles, aiki a cikinta akwai riba babba don za ka ci halas dinka ita kuma hukumar masakar za ta baka hakkinka don ba ta wasa da hakkin ma’aikacinta don ka ga gidan da nake cikin nan da kudin

aikin masaka na same shi.

Kuma yanzu haka a cikin Funtuwa ma’aikatan masaka da dama ne suka samu muhalli a cikinta kuma rashinta masifa ce ga al’ummar yankin Funtuwa. kuma sirrin dorewar wannan masaka shi ne, ba ta ha’inci wajen aiki don duk ma’aikacin da aka kama da ha’inci lallai korarsa ta ke yi.


Advertisement
Click to comment

labarai