Connect with us

LABARAI

Har Yanzun Akwai Katin Jefa Kuri’a Milyan 7.9 Da Ba A Karba Ba –INEC

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, (INEC), ta ce, a yanzun haka akwai katunan jefa kuri’a guda 7,920,129, wadanda masu su ba su zo sun karba ba a Ofisoshinta na cikin kasarnan.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata takardar bayanai da ta fitar a Abuja, ranar Talata.

Takardar bayanan ta nu na, ya zuwa watan Maris 2018, Jihar Legas ce ta fi yawan katunan zaben da ba a karba ba, inda take da katunan zabe, 1,401,390; sai Jihar  Oyo, 647,586; da Jihar Edo, 449,001, Jihar Kano ita ma tana da katuna, 195,941, a kasa.

Takardar ta nu na Jihar Bauci ce take da karancin katunan zaben da ba a karba ba, inda take da katuna, 15,542, a kasa, sai Jihar  Bayelsa da Flatau, masu katuna, 28,533 da 25,300, bi-da-bi.

Hukumar kuma ta bayyana cewa, ya zuwa yanzun ta raba katunan zaben guda, 351,272, a Jihohi 36 har da babban birnin tarayya, a tsakanin shekarar 2015 zuwa watan Maris na shekarar 2018.

Ta ce, an karbi katunan zaben, 230,175 daga cikin, 351,272 a shekarar 2017 sauran, 121,097 kuma an karbe su ne a shekarar, 2018.

Jihar da aka fi karbar katunan zaben a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018, ita ce, Jihar Anambra, inda aka karbi katuna, 102,264.

Jihohin Kogi da Legas na biye da katuna, 41,174 da 20,002, bi-da-bi.

Jihohin da aka karbi katunan ma fi karanci su ne, Jihohin Zamfara, guda arba’in ne kacal aka amsa, sai Taraba, an amshi guda 158 ne kacal, Bauci, an amshi guda, 558, ne in ji Hukumar.


Advertisement
Click to comment

labarai