Connect with us

LABARAI

Ba Mu Bukatar Jam’iyyar Da Ba Ta Da Manufa Akan Inganta Kiwon Lafiya –Likitoci

Published

on


Daga Abubakar Abba

Kungiyar Kwararrun Likitoci ta Kasa (NMA) ta gudanar taron muhawar wanda bata taba yin irin sa don yin muhawara akan dama da kuma barazanar dake shafar fannin kiowon lafiya kafin zuwan zaben shekarar 2019.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a Abuja a ranar Talatar data gabata.

A cewar shugaban kungiyar na kasa Mike Ogirima,taron wanda ya samu halarcin jam’iyyun siyasa da kafafen yada labarai da ‘yan makaranta da kungiyoyin sa kai da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, ya bayar da damar tattaunawa akan manufofin jam’iyyu da tsare-tsaren da suke dashi na inganta kiwon lafiya a kasar nan.

Ogirima ya ce gaba da cewa, taron shiri ne na inganta kimiyya wanda ake sa ran gudanar dashi a cikin watan Mayu kuma za a yi amfani dashi wajen bai wa masu ruwa dakundi daukar matsayi a Abuja akan zagewar da za a yi na inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan.

Shugaban a taron manema labarai akan shirye-shiryen gudanar da taron na kimiyya wanda shi ne ya yi na karshe a zaman na shugaban kungiyar ya ce,  fannin kiwon lafiya a kasar nan yana cikin tsaka mai wuya kuma fannin na kara fuskantar barazana.

A cewar sa,Nijeriya ta kai matsayin ta 181 daga cikin kasashe 187 akan fannin kiwon lafiya, inda kuma yin rigakafi ya sauka da kashi  saba’in da shida bisa dari a ‘yan shekaru da suka gabata zuwa kashi ashirin da uku bisa dari.

Ya yi nuni da cewar, Nijeriya tana daya daga cikin kasashen da har yanzu ta kasa shawo kan ciwon Foliyo kuma kasar tana akan siradin kara samun mace- macen mutane.

Ya yi nuni da cewa, gaba dayan inshorar lafiya bai wuce kashi biyar bisa dari ba da aka yiwa ‘yan Ni tun a shekarar 2005, inda hakan ya nuna cewar, kasar ta sauka daga matsayin ta tun a binciken da aka gudanar a 2003.

Ya sanar da cewar, “Nijeriya bata bukatar zartarwa ko samar da wani tsari akan fannin kiwon lafiya”.

Ya ce, abin da Nijeriya take bukata ayau shi ne, dagewa wajen mayar da hankali a dukkan matakan iko na kasar don inganta fannin kiwon lafiya.

A cewar sa, “wannan zai faru ne idan an samar da kudi da sayar da hannun jarin fannin da samar da kirkire-kirkire don inganta fanin na kiwon lafiya da kuma sanya takunkumi ga wadanda suke da kunnen kashi.


Advertisement
Click to comment

labarai