Connect with us

KASUWANCI

Sama Da Hada-Hadar Kasuwanci 10,500 Ake Yi Kullum A ‘Computer Billage’

Published

on


Kimanin hada-hadar kasuwanci 10,500, ne ke gudana a duk yini a kasuwar Kwamfuta ta Legas.

Ahmed Ojikutu, Shugaban masu sayar da kwamfutoci da kuma kayan gyaran su, CAPDAN,  na kasa ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a.

Mista Ojikutu, ya ce, kimanin ‘yan kasuwa 25,000 ne suke gabatar da kasuwanci a cikin shaguna 3,500.

“Matasa da kuma manyan ‘yan kasuwa ne ke gudanar da harkokin kasuwanci.”

“Kasuwar ta, ‘Computer Billage,’ tana samar da harajin Naira bilyan 1.5 a kullum.

“Aiki ne mai wahala jagorantar ‘yan kasuwa maza da mata masu yawa karkashin inuwa guda, musamman kasantuwan mafiya yawan su masana ne kuma masu kudi,” in ji Ojikutu.

“Ayyukan kasuwancin da ake gabatarwa da kuma yanda kudi ke canza hannu a Kasuwar namu, za a iya cewa su na da yawa, za a iya cewa cibiya ce kasuwar ta kayan fasahar zamani, kama daga gyaran su, canza masu fasali da makamantan su,” in ji Shugaban na CAPDAN.

Ya ce, a yanzun kasuwar tana hada kai sosai da sassan hukumomin gwamnati fiye da a baya.

Ya ce, kungiyar na su kuma tana aiki tare da hukumar sadarwa, NCC, da kuma hukumar ci gaban fasaha da kimiyya, NITDA.

“Gwamnatin Jihar Legas ta taimaka mana sosai, amma dai har yanzun muna neman karin taimako daga gare ta, domin kimiyya da fasaha shi ne abin da zai iya ciyar da Nijeriya gaba a halin yanzun.

Ya ce, shirin da gwamnatin ta Jihar Legas ta ke yi na sake wa kasuwar na su matsuguni zai tabbata ba da jimawa ba, inda ya ce, sabon matsugunin zai kasance tsararre ne sosai.

Ojikutu ya ce, sabon wurin zai kasance yana da hanyar shiga yanar gizo ta WiFi, kai tsaye, da kuma babban janareta da zai baiwa kasuwar hasken lantarki bakidayanta.

Ya kara da cewa, kungiyar na su tana fafutukar ganin muna samar da wayoyin hannu na kanmu ne a Nijeriya, suna kuma hada kai da hukumar ta NCC, domin samar da yanayin da za a rika horar da matasa yanda za su zama kwararru.

“Rashin ilimi ne ke hana mu iya kera wayoyin hannu a Nijeriya. Ya kamata mu matsa daga masu amfani da wayoyin hannu, mu zama masu kera wayoyin.

“Kamar yadda muka dage wajen ganin mun horar da matasan mu yadda za su kera wayoyin hannun, muna fatan kuma za mu iya haifar da kwararrun masu hada wayoyin.

Ya ce, kasuwar sabbin wayoyin tana ta kara bunkasa ne a cikin kasar da kashi 95, na ‘yan Nijeriya masu bukatar wayoyin duk sabbi suke nema.

 


Advertisement
Click to comment

labarai