Connect with us

LABARAI

Zan Bayar Da Goyon Baya Ga Majalisar Masu Ruwa Da Tsakin Arewa –IBB

Published

on


Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida, ya yabawa kungiyar Shugabannin Arewa, (NLSA), kan kokarin su na ganin ci gaban kasarnan, ya kuma alkawarta goyon bayan shi ga kungiyar na su.

Babangida, ya yi wannan alkawarin ne Jiya, sa’ilin da wakilan kungiyar suka ziyarce shi a Minna.

Babangida, ya bayyana kungiyar a matsayin, “Kungiyar da ya kamata a karfafe ta,saboda dagewar ta na samar da hadin kan ‘yan kasannan, da kuma kawo gyara a cikin kasar.

“Za mu karfafi abin da ku ke yi, mu kuma mara maku har ku ci nasara.”

Shugaban kaungiyar, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana kungiyar a matsayin wacce ba ta siyasa ce ba.

Ya ce, duk dan Arewa yana iya shiga kungiyar, ba tare da la’akari da kasancewar kabila ko Addinin  ko Jam’iyyar shi ba.

Ya kara da cewa, “Kasancewar mu ba Jam’iyyar siyasa ba, manufar mu ita ce, samar da fahimtar juna da hadin kai.

Yakasai ya ce, an kafa kungiyar ce ranar 10 ga watan Fabrairu 2018. Daga nan sai kungiyar ta nada IBB a matsayi na Uban kungiyar na ta.

Kadan daga cikin wakilan kungiyar sun hada da tsohon Shugaban Majalisar wakilai, Alhaji Ghali Na’abba, da tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu.


Advertisement
Click to comment

labarai