Connect with us

LABARAI

Yawan Masu Rubuta Jarabawar NECO A 2018 Ya Karu

Published

on


An samu karuwar masu zana jarabawar shiga makaratun hadin ka na gwamnatin tarayya da hukumar shirya jarabawa ta NECO ke gudanawa a wannan shekarar fiye da yadda abin yake a shekarar 2017, a wannan shekarar dalibai ne 79,887 suka zana a shekarar 2017 kuwa dalibai 78,378 suka shiga jarabawar, an kuma ba dalibai masu nakasa kulawa na musamman a wannan shekarar.

Karamin Ministan ilimi, Anthony Anwukah, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Asabar a lokacin da yake zagayawa cibiyoyin zana jarabawar a yankin babban birnin tarayya Abuja (FCT).

Ya ce, dalibai masu hankoron shiga kananan makarantun sakandare (JSS) na 104 Unity Colleges guda 104 da muke das u wanna da hukumar NEC Ota shirya a fadin tarayya kasar nan, an gudanar da shi ba tare da wani matsala ba.

Mista Anwukah ya lura da cewa, an gudanar da jarabawar cikin yanayi mai aminci, ya kuma yaba wa hukumar NECO a bisa wannan gaggarumun aiki da suka yi.

Ya kara da cewa, a wannan shekarar a ana gudanar da jarabawar ne a dukkan fadin kasar ba kamar shekarar 2017 da ba a gudanar da jarabawar a jihar Borno da Adamawa ba saboda harkokin ‘yan tayar da kayar baya.

“Na zo ne domin ganin yadda ake gudanar da jarabawar, ina son ganin ko wurin da akr gudanar da jarabawar ya cancanci a yi jarabawa a ciki ko a a, na samu tabbacin lallai ana gudanar da jarabawar a yanayin day a kamata na kuma ji dadin abin dana gani a halin yanzu”

Ya kuma kara bayyana cewa, yawan wadanda suka samu nasara a jarabawar ne zai nuna yawan daliban da za a dauka zuwa makarantun gwamnatin tarayya dake fadin kasar nan”

A nasa jawabin, magatakarda hukumar NECO, Charles Uwakwe, a ana gudanar da jarabawar ne a fadin tarayyar kasar nan a lokaci daya tare da cikkaken tsaro. Ya ce, dalibai daga jihar Legas su suka yawa, in da suka kai 25, 800 yayin da jihar Zamfara ce take da dalibai mafi karanci da dailibai 28.

“A nazarin da nayi aikin yana tafiya cikin tsari, Minista ya ce mu ba kowa kafar gwada sa’arsa saboda kada a hana kowa samun daman shiga makarantun”

“Babu wani matsala daga jihar Barno sune ma suka fi yawan dalibai a Arewa maso Gabas da dalibai 79,887, jihar Legas ked a dalibai mafi yawa na 25,800 yayin da jihar Zamfara ked a mafi karancta”

Ministan ya kuma ce a wannan shekarar mun yi tanadi na musamman ga dalibai masu nakasa saboda suma su samu daman shiga makarantun Unity na gwa,mnatin tarayya.

Ya ce, ma’aikatan ilimi zata dauki dalibai ne ta cin jarabawar da suka yi.

Wakilinmu daya zagaya don lura da yadda aka yi jarabawar ya lura da cewa, a fara gudanar da jarabawar a kan lokacitare da halartar jami’an tsaro.

An gudanar da jarawar ne cikin kwanciyar hankali a Gobernment Secondary School, Wuse Zone 3 da Gobernment Secondary School, Garki da Tudun Wada Secondary School in Zone 4 duk a cikin garin Abuja. An kuma lura da cewa, daliban sun fito jarabawar ne a cikin kayan sun a makaranta tare da rakiyar iyayensu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai