Connect with us

LABARAI

Theresa May Ta Bukaci Kasashen Commonwealth Su Yarda Da Auren Jinsi Daya

Published

on


Firayim Ministan Birtaniya, Theresa May, ta bukaci Najeriya da sauran kasashe a cikin Commonwealth su yarda da auren jinsi daya. Yayinda yake jawabi a taron farko na hadin gwiwa, a taron shugabannin Commonwealth a garin Westminster a ranar Talata, Firayim Ministan tace bai kamata a samu wata dokar da za ta haramta auren jinsi daya a tsakanin kasashen dake Commonwealth.

A cewar ta, ta fahimci cewa mafi yawan dokoki game da auren jinsi daya an kafa sune a  Ingila, ta kara da cewa wadannan dokoki ba daidai ba ne a wancen lokacin, kuma ba daidai ba ne a yanzu. Ta kara da cewa, “A dukan faɗin duniya, dokoki masu nuna bambanci da aka yi shekaru da yawa da suka wuce suna ci gaba da shafar rayukan mutane da yawa wanda mafi yawan su matasa ne.

Ta ci gaba da cewa,” a matsayin Firayim Minista Birtaniya, na yi matukar damuwa da bakin ciki da gabatar da dokokin nan, dole ne mu girmama al’adunmu da al’amuran juna.

Kamar yadda aka bayyana a cikin yarjejeniyar Commonwealth. “Babu wata kasa da  ya kamata ya fuskanci bambanci ko zalunci saboda matsayin ta ko kuma wanda take so.

Sa’annan kuma Birtaniya ashirye take ta taimaka wa kowacce kasa da take so ta gyara dokokin auren jinsi daya.


Advertisement
Click to comment

labarai