Connect with us

RAHOTANNI

Miliyoyi Sun Halarci Maulidin Shehu Inyas A Abuja

Published

on


A ranar Asabar din da ta gabata ne, 15 ga watan Rajab, miliyoyin jama’a a fadin kasar nan da wasu kasashe suka yi wa birnin tarayyar Nijeriya kawanya domin gudanar da gagarumun maulidin tunawa da ranar haihuwar Shehu Ibrahim Inyass (R), wanda suka saba yi duk shekara. Wannan maulidin shi ne karo na 42 da ake gudanar da wannan maulidin a Nijeriya.

Wakilinmu ya labarto mana cewar tun kafin ranar ta Asabar, Abujan ya samu cikowar jama’a musamman ‘yan darika daga sassa daban-daban na Nijeriya inda suka yi gagarumar addu’a ta musamman wa kasar nan domin wanzar da zaman lafiya da kuma samun shuwagabanai na gari.

Babban taron maulidin na kwanaki biyu, wanda ‘yan Darikar suka yi cincirido a babban Massalacin kasa a ranar Alhamis da yammaci inda suka fara yin addu’o’I na musamman har zuwa Juma’a, a yayin da kuma a ranar Asabar din ne suka nausa babban filin wasa da ke Abuja Eagle Skuare domin gudunar da babban maulidin na Shehu Inyass wanda ya kunshi baki daga kasashe sama da 16 a fadin duniya.

Maulidin Shehu Inyass din wanda ya hada fuskokin manyan Shehunan, Malamai, shuwagabanai, ‘yan siyasa da kuma dandazon mabiya Darika daga sassan duniya, cikin manyan bakin da suka halarta har da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, wanda ake tunanin zai tsaya takarar shugaban kasa, tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Da yake jawabi a wajen gagarumar taron, babban Malamin darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci dukkanin mabiyansa da sauran ‘yan Nijeriya da su tabbatar da mallakar katin zabe na dindindin wato (Permanent Boter Cards) domin fuskantar zaben 2019 da ke tafe.

Shehu Dahiru Bauchi ya bayyana cewar ta hanyar mallakar PBC ne kadai mutum ne da iko gami da zarafin zaben dukkanin wanda yake so a kowani lokaci da zarar aka fara hidimar zabe, Malamin ya misalta cewar katin zaben siyasa a matsayin wata makami mai karfi ga kowani dan kasa.

Dahiru Bauchi ya bayyana cewar katin zabe a matsayin wata makami mai karfin gaske da kowani dan kasa zai yi amfani da ita wajen zabar nagartaccen shugaban da ya dace ya mulkesa a bangaren shugabanci daban-daban.

Daga nan kuma ya kirayi dukkanin mabiyansa da su tabbatar da mallakar katin zabe na dindindin domin zabar mutumin da suka tabbatar da nagartarsa, wanda zai yi musu aiki na gari a kowani lokaci,

Ya ce, ta hanyar zabe ne kowani dan kasa zai kwaci ‘yancinsa gami da fitar da damuwarsa ta fuskacin zabe.

Shaikh Bauchi ya bayyana cewar manufar shirya maulidin dai domin nuna godiya wa Allah da samuwar waliyin Allah a yankin Afirka Sheikh Ibrahim Niyass daga kasar Senegal.

Ya bayyana cewar Shehu Ibrahim Inyass ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gabantar da addinin musulumci, hade da koyar da musulunci a fadin Afirka da duniya baki daya.

Ya kuma bayyana cewar suna amfani da irin taron wajen yin addu’o’I na musamman wa kasar nan domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa a kowani bigire, ya kuma kara da cewa addu’a ita ce hanya daya tilau na samun mafita a kan kowace kalubalen ko matsalolin da suke fuskantar kasar nan.

Da yake jawabi a wajen maulidin, shugaban Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari ya jinjina wa kokarin shuwagabanin kungiyar darikar Tijjaniyya wajen kokarin wanzar da zaman lafiya a fadin kasar nan ta fuskacin yi wa kasar addu’a kan matsalolin da suke addabar Nijeriyar a kowani lokaci.

Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya tabbatar da cewar Shehu Inyas ya bayar da gagaruman gudunmawa wajen daukakar addinin Islama musamman a yankin Afirka, Asia da kuma yankin Europe.

Ya kuma aniyar gwamnatin tarayya na ci gaba da bayar da gudunmawa wajen karfafar zaman lafiya da ci gaban jama’a a kowani lokaci a wannan kasar ta Nijeriya.

Babban Limamin Markaz Faidal Islamic Foundation, da ke Suleja, Shiek Abubakar Musa Kwamba, ya bayyana cewar ‘yan Tijanniya suna matukar girmama ranar haihuwar Sheik Ibrahim Nyass domin nuna murnarsu a kan samuwar tasa.

LEADERSHIP A YAU ta labarto cewar kadan daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da Khalifan shehu Tijjaniyya  wanda kuma da ne ga Sheikh Ibrahim Nyass, Sheikh Ahmad Tijjanni Nyass daga kasar Senegal, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin Mallam Adamu Adamu, ‘yan majalisu, gwamnoni, wakilin Sarkin Musulmai, tsohon dan majalisar Ghali Umar Na’aba, da sauransu.

Wasu daga cikin kasashen da suka hallarci taron sun hada da Morocco, Senegal Tanzania, Egypt, Libya, Britain, Jamus , Aljeriya, Masar, Sudan, Chadi, Ghana, Kamarun da wasu daga kasashen European.

Wakilinmu ya labarto cewar birnin tarayyar Nijeriya ta cika ta batse, inda ‘yan darikar suka cike kowani lunguna da sakonan titin Abuja a cikin wadannan kwanaki biyun.

Tun da fari ma, Dahiru Bauchi ya bayyana cewar ita maulidi ana yin tane domin nuna godiya wa Allah da samuwar bayin Allah na gargaru da kuma salihan bayi, ya bayyana cewar suna taron tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, don haka ne kuma suke taron tunawa da ranar da aka haifi magadansa, ya ce soyayya da godiya wa Allah ce manufarsu a kowace lokaci na yin irin wannan taron.

 


Advertisement
Click to comment

labarai