Connect with us

RAHOTANNI

Kafin Lemu: Garin da Arziki Ke Neman Mutane

Published

on


A yanzu haka da Gwamnatocin wasu Jihohin ke Kokarin ganin sun mayar da hankali wajen zakulo albarkatun kasa da Allah ya shimfide a wasu jihohin arewacin Najeriya, musamman ganin yadda ake yiwa al’ummar wannan yanki gorin man fetur da Gwamnatin tarayya ta dogara dashi wajen raba kudaden gudanarwa ga Gwamnatocin Jihohin Najeriya. A wasu garuruwan a iya cewa rashin sani yasa kaza kwana kan dami, domin kuwa akwai wuraren da Allah ya jibge ma’adanan da idan akayi amfani dasu wajen hako su, ko shakka babu an daina maganar man fetur baki daya.

Garin Kafin Lemu gari ne dake kasar Ningi a Jihar Bauchi wanda ya yi iyaka da Garin Magami dake cikin yankin karamar Hukumar Sumaila a Jihar Kano ta bangaren arewa, sannan kuma ta bagaren yamma garin ya yi iyaka da karamr Hukumar Tudun Wada, a gabas  kuma ya yi iyaka da karamr Hukumar Birnin Kudun Jihar Jigawa. Garin Kafin lemu wanda masarautar garin ake kiranta da sunan Parda, Allah ya albarkaci garin da Jajirtaccen Hakimi mai suna Alhaji Usman  Idris Parda wanda ya samu amsa  tambayoyin wakilinmu cikin ‘yan Mintuna biyar.

Alhaji Usman Idris Parda haifaffen garin Gatangar Warji dake karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi cikin Shekara ta  1967, ya shiga makarantar Allo kasancewar bamu shiga ilimin zamani da wuri ba, inji Hakimin na Parda.  Bayan na samu abinda na samu na shiga makarantar firamare, nayi sakandire harkuma na samu shaidar diploma , daga nan na fara aiki da wani Banki a matsayin akawu, wanda nayi aiki tsawon shekara biyu daga 1978-1989.

Sai na wuce zuwa Jami’ar Maiduguri inda na samu digiri na na farko, na gudanar aikin yiwa kasa hidima a wani banki a Jihar Kaduna, wanda sai da na kai mukamin Akanta har kuma na zama  Manajan darakta.

Ya ciga da cewa Mahaifina  wanda alokacin shi ne dagacin Parda Allah ya karbi rayuwarsa, hakan tasa al’ummarmu suka matsa cewar sai na dawo na gaji mahaifin nawa, aka nada ni amatsayin dagacin Parda a shekara ta 1998. Bayan nan ne kuma alokaicn mai Gwamna Malam Isah Yugudu ya shirya samar da karin masarautu, Allah ya kaddara akayi wannan masarauta dana ke rike da mukamin dagaci, aka daga likkafar ta ta koma Kasar Hakimi wanda aka nada ni amatsayin Hakimin Parda.  Mukamin da na ke rike dashi har zuwa wannan ziyara da wannan Jarida mai albarka da ta kawo garin Kafin Lemu dake masarautar Parda.

Duk da wannan bunkasar da kuma wadataccen ilimi da kuma matsayin Hakimta da wannan mutun yake dashi, hakan ba ta sa shi rungumar mulkin amatsayin abin tinkahon da kila zai sa takalmin karfe domin murkushe mai karamin karfi ba, bilhasali ma ko da Jaridar LEADERSHIP A Yau ta isar fadar Hakimin muka bukaci ayi mana iso, da ya fito mun dauka wani ne daga  cikin fadawansa saboda walwala.

Yakana, kaskan da kai da kuma budaddiyar fuska ga al’ummar da yake wakilta. Kasancewarsa  gogaggen mai lilimn zamani da kuma ilimin addini, ya tabbatarwa da kansa cewa bai kamata basarake ya dade kafarsa kawai sai mulki ba, kamata ya yi ya bude kofarsa domin gayyatowa al’ummarsa duk wani tsari da zai kawowa garin nasa ci gaba.

Garin Kafin Lemu garin ne kamar yadda idonmu ya gane mana wanda Allah ya horewa kogi mai gudana wanda ya taso tun daga tabkin Tiga dake Jihar Kano, ya ratsa T/Wada, ya shiga Bura, ya shigo Kafin Lemu har sai da ya dangana da Kafin Gana. Hakan ta baiwa al’ummar wannan yanki damar gudanar da harkoki Noman rani da damina, sannan kuma wanann Gari ana noma Auduga iya ganinka, Shinkafa, Waken Soya, Gyada da sauran manyan amfanin gona da duniya ke alfahari dasu. Kamar yadda cikin bayanin Hakimin ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau cewa wannan gari na Kafin Lemu gari ne da arziki ke neman jama’a, domin  akwai manyan Duwatsu tun daga Katangar Warji suka ratsa ta Gwaram, Bura zuwa Garin Kafin Lemu.

Akwai ma’adanai kamar zinare, duwatsun kawa da sauransu masu yawan gaske shimfide wannan yanki, kenan Karin maganar Bahaushe da ke cewa rashin sa ni ya sa kaza kwana kan dame.

Sakamakon wannan manyan labarkatun kasa da Allah ya albarkaci wannan gari dasu yasa Hakimin Alhaji Usman Idris Parda mayar da hankali domin ganin ya gayyato masu harkokin noma irin na zamani da kuma masu sha’awar zuba jari ta fuskar hakar ma’adanai domin shigowa wannan yanki domin gudanar da harkokinsu, hakan zai taimaka kwarai da gaske wajen bukasar tattalin arzikin kasa, samar da sana’un dogaro da kai alokaci guda kuma Gwamnatin karamar Hukuma, Jiha da kasa baki daya suka kara samun isassun kudaden shiga.

Yanzu haka Garin Kafin Lemu wanda ya shahara wajen Noman audugu, Rake, Shinkafa, Waken Suya, Gyada an tsara samar da guraren noma ga masu sha’awa sannan kuma manoman kauyen wayayyune, aduk lokacin da aka gabatar masu da wani sabon tsarin noma a shirye suke da karbarsa kuma suna wadatattun filayen noma wanda suke bada aro, haya ko kuma su noma da kansu.


Advertisement
Click to comment

labarai