Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Alkawarin Sake Sakin Sunayen Barayi

Published

on


A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake sakin wasu sunayen na mutanan da take zargi da tsiyata kasarnan.

An dai yi ta sukan sunaye kashi biyun da ta saki a baya da cewa duk ‘yan adawarta ne na Jam’iyyar PDP.

Ba wanda aka daure cikin su, wasun su ma an yi masu shari’a, wasun su ma ko tuhumar su da aikata laifi ba a yi ba.

A jawabin da ya saki a Legas ranar Lahadi, Ministan al’adu da yada labarai, Lai Mohammed, cewa ya yi, tun lokacin da aka saki jerin sunayen biyu na barayin da ake zargi, an yi ta kokarin suka da shafawa gwamnatin tarayya kashin kaji, kan ta daina sakin sunayen.

“Marubutan karya da kafafen yada labarai da yawa sun ta sukan gwamnatin tarayya kan sakin sunayen. Da yawa suna zargin sanya siyasa cikin yakin da ake na cin hanci da rashawa, ta hanyar sakin sunayen, sam ba mu yarda da sukan na su ba.”

“Ba mu da ikon daure kowa. Wannan aikin kotuna ne. amma muna da ikon shaidawa ‘yan Nijeriya wadanda suka wawashe masu dukiyar su, ta hanyar gabatar da kwararan shaidu, mu abin da muke yi kenan,” in ji shi.

Sai dai sabanin abin da Lai Mohammed din ne ya fada, gwamnati tana da karfin kamawa da hukunta kowa da ake zaton ya saci dukiyar al’umma, kuma ta na yin hakan. Amma cewan da ya yi hakan aikin Kotuna ne, gaskiya ne.

“Duk masu maganan an sanya siyasa cikin lamarin, suna so su hana gwamnati sake sakin sunayen ne, in mutum dubu za su yi rubutun sukar mu, hakan ba zai hana mu sake sakin sunaye a karo na uku ba,” in ji Lai.

Ministan, ya kalubalanci duk wanda yake jin kage aka yi ma shi da ya nufi Kotu, maimakon ya tsaya yana zage-zage.

Jim kadan, kafin wannan bayanin da Lai Mohammed, ya aikewa kafar sadarwa ta, PREMIUM TIMES, fadar gwamnati ta saki wani bayanin, inda Shugaba Buhari ya sake zargin gwamnatin PDP, da tsiyata Nijeriya.

Inda Buhari ke cewa, lalata tattalin arzikin da aka yi lokacin waccan gwamnatin ya yi yawa, amma gwamnatin sa na kokarin kwato wasu daga cikin abin da aka sata, amma ya ce, bai yiwuwa a iya kwato duka.

“In a ce sun yi aiki da kashi 50 na kudadan Mai da muka samu lokacin da yake dala 143 kan ganga guda, muna kuma fitar da ganga milyan 2.1, a kullum, da ‘yan Nijeriya sun ji dadi.

“Za ka iya yin shuka a kan hanyoyinmu, domin duk an yi watsi da su. Satar ta yi yawa, har ma sun kasa boye ta sosai.

Buhari, ya yi wannan maganan ne daga London, lokacin da yake maraba da wasu magoya bayansa da suka kai ma shi ziyara karkashin jagorancin, Mista Charles Sylbester.

Da yake na shi jawabin, jagoran kungiyar, Mista Charles Sylbester. Cewa ya yi, kungiyar na su tana farin ciki da irin ci gaban da gwamnatin Buhari din ta kawo ya zuwa yanzun.

Ya yi nu ni da cewa, Buhari, ya gama da yawancin matsalolin da ya taras, musamman a sassan Noma, saukake hanyoyin yin ayyuka, yaki da cin hanci da rashawa, samawa matasa ayyuka ta hanyar shirin N-Power, da kuma samar da asusun baidaya, (TSA), da sauaran su.

Ya kuma yabawa gwamnatin kan yakin da take yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas, da kuma shelantawan sake tsayawa takara da ya yi a 2019.

“Mun kuma yaba gaggawan da gwamnatin ka ta yi na amso ‘yan matan Dapchi. Hakan ya nu na lallai kai Janar ne.

“Allah da Ya warkar da kai da ba ka lafiya, Shi ne zai ba ka nasara a 2019. Kai Janar ne da ba ka shakkan fada da Janarori ko wadanda ba Janar din ba.”


Advertisement
Click to comment

labarai