Connect with us

MAKALAR YAU

Falsafa: Tsafi, Duba Da Rufa-ido (I)

Published

on


[email protected]                    +2349039128220 (Tes Kawai)

Tsafi:

Karatun tsafi da yadda yake yana bangaren “Metaphysics” a Falsafa. Ya wuce ilimin Kimiyya (Science) domin shi yana karatun bayan dabi’a ne (Beyond the nature) ita kuma kimiyya na karantar dabi’a ne (nature). Kimiyya za ta gayamaka daga 1 sai 2 amma “Metaphysics” shine zai gayamaka meyasa daga 1 sai 2. Kimiyya za ta gayamaka daga A sai B amma “Metaphysics” na binciken meyasa daga A sai B. Don haka kimiyya ba za ta iya karantar tsafi ba don haka ta sanyashi a cikin “Pseudoscience” domin hakikar gane tsafi sai a “Philosophy”.

Tsafi dadadden abune a tarihin dan adam da ya samu ci gaba a shekaru dubbai da suka wuce. Mutanen Syria, Egypt, Babylons, Nabataens da Chaldaens sune suka samu cigaba a bangaren wannan sana’a. Bayan zuwan musulinci an samu wasu daga malamai da suka karanci sihiri da tsafi don su san hakikarsa a babin ka san sharri ba don ka aikata sharri ba. Jabir bn Hayyan, wanda babbane a cikin masana kimiyya (Alchemy), ya karanci tsafi har sai da aka rika kiransa da “Chief sorcerer of Islam”. Sannan a Spain an samu irinsu Maslama bn Ahmad Almajiristi da har littafi ya rubuta akan tsafi mai suna “Ghayah” wanda yake tattare da abubuwan mamaki kwarai da gaske!

Aikata tsafi haramunne a addinin musulinci saboda cutarwar da yake wa mutane kuma yana bukatar, a mafi yawan lokaci, mutum ya dogara ga wanin Allah a zahiri. Matsafa suna fara iya tasarrufi da ruhinsu kafin su aikata duk abin da suke. Wanda zaiyi tsafi yana bukatar yazama mai iya juya ruhinsa (soul) ta yadda jikinsa ba zaiyi tasiri ba a lokacin da yake aikata tsafin. Tamkar mutumin da yake hawa dogayen gidane (skyscrapers), idan yana so yayi gudu ya tsallaka daga wannan gidan zuwa wancan mai tsawon gaske to dole sai ya cire tsoron da yake ransa kafin ya tsallaka. Rashin haka zai iya sanyawa yayi karkarwa ya fado. Kamar wanda yake tafiya a tsaye akan igiyar da aka daure tsakanin dogayen gini biyu. Idan mutum yaji tsoro a lokacin da yake tafiya akan igiyar to shikenan sai yayi karkarwa ya fado, amma idan baiji tsoro ba to zai iya tasarrufi da jikinsa ya cigaba da tafiya bai fado ba. Irin wannan hanyar ita take sanyawa matsafa suna iya tasarrufi da jikinsu ta hanyar sarrafa ruhinsu gurin faruwar wasu abubuwan na ban mamaki. Idan mutum ya kware wajen iya tasarrufi da ruhinsa to anan zai iya tasarrufi da abubuwa dayawa a cikin dabi’a.

Masu aikata “sorcery” ba su fiye amfani da wani abu wajen yin tsafinsu ba. Ga wanda ya kalli film din Marlin wanda yake iya tasarrufi da idonsa wajen tsafi to wannan shine “sorcery”. Masu “witchcraft” sune bokaye da suke amfani da wasu abubuwan na itatuwa ko dabbobi da suke ganin alakarsu wajen aikata wani lamari da ruhinsu a lokacin da suke tsafin. Irin wadannan sune masu cewa akawo itace kaza ko farar tsuntsuwa wajen aikata wani lamari. Na taba karanta yanayin wani tsafi mai ban tsoro da ya ce a jika gawar mutum da man ridi har tsawon kwana 40 a rika yagar naman da ya ragargaje ana ci a lokacin da ake tasarrufi da ruhi, to ta nan mai tsafin duk abin da ya fada ya ce zai faru to a kaso 100 za a samu 80 ya faru! Irin wadannan matsafan malaman musulinci sukace a kashe duk mai yi.

Banbancin mai tsafi da mai mu’ujiza ko karama shine, shi mai mu’ujiza ko mai karama an san shi da kyawawan dabi’u (ethics) kuma har lokacin da yake aikata mu’ujizar ko karamar bai dena aikata kyawawan dabi’u ba. Shi kuma mai tsafi an sanshi da munanan aiyuka da kuma aikata wasu abubuwan da ake ganin nutsattsen mutum ba zai aikata ba domin har kisa sunayi akan hanyar tsafinsu. Abin da yasa wasu daga masana tsafi suke yarda da Annabawa shine gane cewar hanyar tsafi daban da ta Annabta. Wannan shine yasa matsafa suka yarda da Annabi Musa saboda sun gane cewa hanyarsa daban da tasu. Abin da yasa ingantattun mu’ujizozin Annabi Muhammad (saw) ba su zamo tsafi ba saboda larabawa sun riga sun sanshi da kyawawan dabi’u har suka rika kiransa da sunan Amintacce.

Duba:

Duba ta hanyar taurari shi ake kira da “Astrology” (da banbanci da “Astronomy” da take nufin kimiyyar taurari), shi kuma duba ta hanyar zanen kasa (ramli) shi ake kira da “Geomancy”. Wadannan ilimai, kamar na bayansu, suma suna da asali daga mutanen Hindu da asalin ilimin za a sameshi a cikin manyan litattafnsu kamar Beda, inda aka samo “Bedic astrology”, da kuma abubuwan da aka rawaito a litattafansu a yaren Sanskirt. Tun a zamanin Greek ana hade ilimin “Astronomy” da “Astrology” guri guda. Ptolemy a cikin littafinsa da yayi a ilimin falaki (Astronomy) ya hada da bayanin “Astrology” da kuma yadda yake tafiya a fahimtarsa. Yana fadar cewa, wasu abubuwan suna faruwane daidai da yanayin tafiyar taurari da kuma tafiyar rana da watanni. Don haka idan aka san yadda taurari suke to za a iya gano yadda gaba za ta kasance. Ta haka zamu gane cewa ilimin taurari ya gangaro musulinci daga iliman Greeks ne.

Ibn Khaldun a cikin Mukaddima, yana cewa akwai bukatar asan cewa babu wani bincike na hakika da yake tabbatar da tafiyar taurari da kuma faruwar wasu lamura. Watakila wannan shine zai bamu nasarar da za ta iya nunamana ma’anar cewar Manzon Allah (saw) rana da wata basa kisfewa saboda mutuwar wani (ko rayuwarsa). Wato dai tafiyar falaki bata nuna wani abu “supernatural” kamar na tsafi ko bokanci ko kuma faruwar wani abu anan gaba. Sir Issac Newton, kamar yadda aka rawaito a cikin littafin “Cambridge Companion to Newton”, ya bada labarin cewa ya tattauna da wani masanin ilimin taurari (Astrology) sai yake gayamasa hakikar ilimin ba gaskiya bane amma hanyar cin abincinsu ce!

Masana halayyar dan adam (psychologists) sun tabbatar da cewa abin da yasa mutane suke aminta da gaskiyar ilimin taurari shine yadda suke ganin abu ya faru bayan an fadamusu zai faru. A hakikar lamari ba faruwa yake daidai da yadda aka gayamusu ba. Dan adam yana da saurin manta abubuwane, don haka idan mai ilimin taurari ya ce abu zai faru to mutum mantawa yake har sai wani lokaci can idan abu makamancin hakan ya faru to sai yayi zaton wanda aka taba gayamasa zai faru shine ya faru din. Misali, idan nace mahaifinka zai mutu bayan nayi duba, to mantawa zakai da na taba gayamaka har sai bayan ya mutu din, watakila da karin shekaru masu yawa, kawai sai ka tuno maganar sai kace ai dama na taba dubamaka hakan zai faru! Wannan shine abin da sukace game da yadda abubuwa suke faruwa a ilimin “Astrology”.

Ilimin “Geomancy” shi ake kira da “ramli” ko kuma duba akan yashi (har da biro da takarda duk anayi). Ilimine da ya fita daga rubutaccen ilimin taurari (Astrology), don haka yake da sunaye da kuma salon bincike kusan iri daya da na ilimin taurarin kuma anfi kyautata zaton larabawa sune suka fara yinsa har ya watsu zuwa kasashen Africa da Europe. Shi ilimin ramli digo-digo a ke yi kusan kala 14 don a fitar da wasu abubuwa daga jikin digon. Wanda na koya ina shekara 13 yana aiki ne da zanen da ya fito bayan ka gama zanen da baka kirga ba kuma ka soke biyu-biyu daga cikinsa. Idan 1 ta fito to za a aunata da daidai bukatarka, haka ma idan biyu ta fito. Akwai ababan mamaki a cikin ilimin da suke faruwa amma dai shima ana dorasune kamar yadda ake dora sauran iliman Astrology.

Akwai ababan mamaki da suke faruwa a cikin irin wadannan iliman wadanda har yanzu kimiyya ta kasa gano ya hakikarsu take. Wasu abubuwan kamar “Telepathy”, “Entanglement”, “PSI” da sauransu har yanzu suna bawa masu kimiyya mamaki dukda suna dorasu a babin “Pseudosciences”. Yadda aka iya gano “Kuantum entanglement” to ana zaton za a iya fahimtar wasu abubuwan irin wadannan da tafiyar lokaci. Zamanin amfani da “Classical Physics” na Newton da ya doru akan lissafin Euclid ya wuce. Yanzu muna kan “Kuantum Mechanics” wanda karyata abu tafarar daya don dogaro da kimiyya (classical physics) na nuna raunin mutum a sanin kimiyyar. Ana bukatar bincike na sosai akan abu kafin a karyatashi. Yanzu muna kan “super string theory” wanda ya ce duniya tana da “10-dimensions” maimakon 3-dimensions ko 4-dimensions da Einstein ya kawo! Hankali zai rude bai gano hakikar abubuwa masu “10-dimensions” ba amma hakan baya nufin cewa “super string” karyane don kawai baka fahimci yadda yake ba.

Abu Hamidil Gazhali, a cikin “Almunkidh” yana magana akan “secrets of numbers”, yana fadin cewa akwai abubuwan mamaki a cikin wasu lambobin. Ya bada hoton wasu lambobi da ya ce an kasa gane sirrinsu. Lambobine kawai a jere amma idan aka haskawa mai ciki a lokacin da take nakuda sai aga bata shan wahala sosai! Ibn Khaldun ya fadi wasu lafuza da yaren “Armenians” inda ya ce indai ya karantasu to sai ya yi mafarkin abin da yake so! Abubuwan da ban mamaki ta yadda ake bukatar ayi zurfaffen bincike akai. Irin wannan to dasu aka dora iliman “Numerology” da karanta zanen hannun mutum ko kirgen da a ke yi da carbi.

Za mu ci gaba

 


Advertisement
Click to comment

labarai