Connect with us

LABARAI

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Yara Fiye 1,000 Tun Bayan Sace ’Yan Matan Chibok

Published

on


Akalla yara fiye da 1,000 kungiya Boko Haram tayi garkuwa dasu tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok da suka yi shekara 4 da suka wuce, Inji kungiyar majalisar dinkin duniya ta UNICEF.

Shekara 4 ke nan tun bayan harin da yan ta’aada suka kai makarantar Chibok inda suka sace yanmata 276, kungiyar  UNICEF ta ci gaba da kiran Lallai a saki yan matan tare da kawo karshen hare haren da ake kai wa makarantu  a fadin yankin.

Fiye da matan Chibok 100 ne har yanzu ke a hannun yan ta’aada ba tare da an samu kwato su na, har yanzu majalisar dinkin duniya da ci gaba da sa kiran a sako su da gaggawar.

“Zagayowar shekara 4 da sace yan matan Chibok yana kara tuna mana cewar har yanzu yara sashin Arewa mask Gabas na ci gaba da fuakantar hare hare mai girman gaske” Inji Wakilin kungiyar UNICEF a Nijeriya  Mohamed Malick Fall.

“Ana ci gaba da kai musu haren taaddacin a gidajensu da makarantu da wurare gudanar da karuwar su”

Harin da aka kai garin Dapchi kwanan nan inda yanmata 5 suka rasa rayukansu nuni ne da cewa wurare kadan ne ya rage wa yara a yankin Arewa maso Gabas, makarantu ma basu tsara daga taaddacin ba.

“Wadannan hare harem akan makarantu dake rutsawa da yara babu dalilin yin haka “ Inji  Fall.

“Yara da na hakkin a basu ilimi da kariya na musamman, dole aji Ya zama wuri dake da aminci daga dukkan nauyin cuta”

Tun da aka fara wanna rikicin a shekarar 9 da suka wuce a kashe Akalla Malama makarantar 2,295 sun kuma lallata makarantu fiye da 1,400.

Har yanzu ba a bude makarantun ba saboda tsananin lallacewar da suka yi da kuma matsalar tsarin Sanya addabi yankin a halin yanzu.

Gwamnatin Nijeriya ta kudiri aniyar tabbatar da tsaro a makarantu da kuma kare su daga hare hare,  kungiya UNICEF na tare da gwamnati a kan wannan kudurin inda gwamnati ke bayar da tsaro Na musamman ga manya da kananan makarantun yankin daga duk nauyin hare hare a yayin rikice rikice.

 


Advertisement
Click to comment

labarai