Connect with us

LABARAI

Azzalumai Ne Suke Tsiyata Nijeriya –Buhari

Published

on


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya zargi wadanda ya bayyana da azzalumai da laifin tsiyata ‘yan Nijeriya.

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi A Laondon, sa’ailin da yake maraba da wata kungiyar magoya bayansa karkashin jagorancin, Mista Charles Sylbester.

Sai dai, ya ce, bisa la’akari da yadda gwamnatinsa ta sami kasarnan, ba komai a asusunta kuma tattalin arzikinta a ruguje, “ai mun dan tabuka.”

Buhari ya ce, barnar da aka yi wa tattalin arziki a lokacin da azzaluman ke mulki yana da yawa, gwamnati na iya kokarinta na kwato wasu daga kudaden da aka sata, duk da ba a iya gano duka.

“In a ce sun yi aiki da kashi 50 na kudadan Mai da muka samu lokacin da yake dala 143 kan ganga guda, muna kuma fitar da ganga milyan 2.1, a kullum, da ‘yan Nijeriya sun ji dadi.

“Za ka iya yin shuka a kan hanyoyinmu, domin duk an yi watsi da su. Satar ta yi yawa, har ma sun kasa boye ta sosai.

Buhari, ya yi nuni da yadda Allah Ya azurta Nijeriya da yawan al’umma da kuma albarkatun kasa, sai ya yi juyayin gazawar da wasu da suka yi shugabanci a baya suka kasa cin moriyar su, wanda ta sabbaba kasawan da gwamnatin sa ta yi na cin gajiyar albarkatun kasar domin ta kyautata rayuwar al’umma.

Sai dai ya yaba wa ‘yan Nijeriyan da ke waje masu kokarin kare kasar su, ya bayyana hakan da sadaukarwa.

Da yake na shi jawabin, jagoran kungiyar, Mista Charles Sylbester. Cewa ya yi, kungiyar na su tana farin ciki da irin ci gaban da gwamnatin Buhari din ta kawo ya zuwa yanzun.

Ya yi nu ni da cewa, Buhari, ya gama da yawancin matsalolin da ya taras, musamman a sassan Noma, saukake hanyoyin yin ayyuka, yaki da cin hanci da rashawa, samawa matasa ayyuka ta hanyar shirin N-Power, da kuma samar da asusun baidaya, (TSA), da sauaran su.

Ya kuma yabawa gwamnatin kan yakin da take yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas, da kuma shelantawan sake tsayawa takara da ya yi a 2019.

“Mun kuma yaba gaggawan da gwamnatin ka ta yi na amso ‘yan matan Dapchi. Hakan ya nu na lallai kai Janar ne.

“Allah da Ya warkar da kai da ba ka lafiya, Shi ne zai ba ka nasara a 2019. Kai Janar ne da ba ka shakkan fada da Janarori ko wadanda ba Janar din ba.”

“Mun shelanta kauna da goyon bayanmu gareka. Yanzun kana ta gyaran barnar da aka yi ne, zuwanka na biyu ne za ka gina sabbin ayyuka,” Inji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai