Connect with us

LABARAI

Annobar Cutar Zazzaben Lassa Ba Ta Bulla A Asibitinmu Ba –FMC

Published

on


Hukumar gudanarwar babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola FMC, ta musanta rahotannin da wasu kafafen sadarwa ke yadawa cewa an samu bullar annobar cutar zazzaben Lassa a asibitin.

Da yake magana da manema labarai a Yola, shugaban sashin ayyuka na babban asibitin Dakta Joel Yohanna, yace asibitin ashirye yake da ya tinkarin bullar kowace irin barazana da ta annoba a jihar.

Yace babu wani rahoton bullar annobar a jihar Adamawa, yace mutumin da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar daga jihar Taraba ya fito, inda aka kwantar dashi a wani karamin asibiti a Yola bisa tsammanin zazzaben cizon sauro ke damunshi.

Yace mutumin ya kwanta tsawon kwanaki hudu kafin amaishe dashi babban asibitin na FMC, kafin daga bisani ya mutumin ya rasu, yace dama an kibe mutumin a wani wurin musamman da’aka tanadar domin kwantar da masu dauki da cutar annobar Ebola, kafin agano mutumin na dauki da cutar zazzaben Bera ne.

Ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin likitoci ko kananan ma’aikatan jinya da suka kamu da cutar wacce dama tun da farko an dauki matakin kariya daga mutumin wanda ya mutu bayan kwanaki hudu a asibitin.

Dakta Joel, yace batun harkoki ya tsaya a asibitin karce kawai, domin komai na tafiya daidai inba a kafafen sadarwa ba, hatta ma’aikatan asibitin basusan wani abu ya faru makamancin haka ba, komai na tafi daidai.

“kaga dai gashi komai na tafiya daidai a asibitinnan, kuma babu batun bullar Lasa Feber a kowani yanki na asibitin, shi marar lafiyar daga asibitin Peace Hospital aka kawoshi nan FMC, kuma mun kibeshi kafin ya mutu.

“kuma mun tuntube iyalan mamacin da ‘yar ‘uwar gyatumarshi, wacce itama muka dauketa zuwa nan asibitin mun kibeta muna bincike akanta haka kuma duk ma’aikatan asibitin da suka dubata suna dauke da kayan kariya domin kaucewa matsalar” inji Joel.

Ita kuwa gwamnatin jihar Adamawa ta bakin kwamishiniyar lafiya ta jihar Dakta Fatima Atiku Abubakar, tace mutumin da ya mutum shine bullar cutar na farko a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Tace tuni gwamnatin jihar ta samar da cibiyoyi da tawagar kwararru daga ma’aikatar lafiyar da sauran masu kwararru a fannin ganowa da sanin annoba da suke wakiltar kungiyar lafiya ta duniya WHO domin bincike kan daidaikun mutanen da mamacin ya’yi mu’amala dasu.

Mutumin da ya gamu da ajalinsa sakamakon kamuwa da cutar dan asalin jihar Adamawa, an bayyana sunanshi da Gabriel Ambe, ma’aikaci a rundunar tsaro ta Cibil Defense (NSCDC) da ke aiki a yankin Gembu cikin karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.


Advertisement
Click to comment

labarai