Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Sace Sakataren  NURTW Tare Da Neman Kudin Fansa A Ondo

Published

on


An sace Sakataren kungiyar direbobi ta NURTW reshen jihar  Ondo Mista Kayode Agbeyangi.

Lamarin ya auku ne duku-dukun ranar Asabar data gabata a lokacin yana kan hanyar sa ta zuwa gun iyalan sa dake jihar Legas.

Motar Agbeyangi an ganta a yashe a gefen babban titin Akure-Ilesa an kuma ruwaito cewar, wadanda suka yi garkuwar dashi sun tuntubi iyalan sa da a basu kudin fansa naira miliyan biyar.

Sai dai, har  ya zuwa hada wannan rahoton iyalan sa basu iya hada wannan kudaden ba..

Shugaban kungiyar ta NURTW dake jihar, ya tabbata da aukuwar lamarain.

Ya ce, an sace shi ne yana kan hanyar sa ta zuwa Legas Kakakin ‘yan sandan ya ce, lamarin ya auku ne a wajen jihar domin ba a kawo wa rundunar rahoto ba.


Advertisement
Click to comment

labarai