Connect with us

SIYASA

Zan Sake Yin Takarar Gwamnan –Gwamnan Jihar Filato

Published

on


Gwamanan jihar Filato, Barista Simon Bako Lalong ya bayyana aniyarsa na neman sake tsayawa takara a zaben 2019.

Kwamishin watsa labarai da sadarwa na jihar Filato, Yakubu Datti ne ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a kan harkar tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar da suka gudanar a Yelwa Club Bukur hedikwatar karamar hukumar Jos ta Kudu ran Juma’a nan da ya gabata.

Ya ce hakika gwamnan ya ayyana aniyarsa na sake tsayawa takara a zaben 2019, kuma ya nemi daukacin al’ummar jihar da su bashi cikakken goyon baya don ya sami damar sake mulkar jihar karo na biyu.

Ya ce, akwi dimbin ayyuka da gwamnan ya fara yi wa al’ummar jihar wanda yake neman a sake zabensa don ya samu kamala su a cikin nasara.

Yakubu Datti, ya gode wa al’ummar jihar bisa kyakkyawar hadin kai dake wanzuwa a tsakaninsu kuma ya ce, irin wannan hadin kai na kara karfafa gwiwar gwamnati ta sami shawo kan dimbin matsalolin da ke damunta.


Advertisement
Click to comment

labarai