KASUWANCI
Za Mu Bada Kulawa Ga Ci gaban Lafiya A Dala -Yan’tandu

Shugaban karamar hukumar Dala Kwamred Ali Ibrahim Yantandu yayi kira ga Gwamnatin kano data taimaka ta sayi gidajenda suke da makotaka da Asbitin shaka tafi na Fuskar Arewa dake kwanar Dala damin mai dashi babban Asibiti.
Shugaban wanda ya fadi haka a wajen bukin bude aikin gyaran asibitin da sanya mata gadaje dan masu haihuwa da kungiyar masu masana.antun harhada magunguna ta kasa reshen jahar Kano suka aiwatar a Asibitin.
Ya ce a lokacinda akazo masa da maganar aikin nan danan ya sami goyon bayan yan majalisar kansilolinsa dan haka itama karamar hukumar tasa hannu a aikin ta samarda karin gadaje a asibitin da ya zama na kulada lafiya da karbar haihuwa.
Kwamred Ali Ibrahim Yantandu wanda nan take ya amince da sauyawa Asibitin suna zuwa Asibitin karbar haihuwa da kulada lafiya na Malam Lawan Danbazau bayan bijiro da shawarar yin hakan ya ce kofarsa a bude take ga duk wanda ya fito da kokari na ci gaban Dala a kowane bangare.
Kwamred Ali Yantandu ya ce dawowarsa shugabancin Dala duk da matsin tattalin arziki yazo da manufa da tsarin yin aikine,badan komai ba saboda Dala Allah ya bata hazikan mutane masana,yankasuwa.malamai, tanada al’umma jajirtattu da sukeda tunanin su taimaka ta hanyoyi daban-daban.
A nata bangaren shugabar kulada lafiya a matakin farko ta karamar hukumar Hajiya Aisha Sani Wali ta bayyana cewa kungiyar ta masu masana’antun harhada magunguna sunyi aiki a asibitin na tsaftaceshi da yin gine-gine da samarda gadon haihuwa wanda za a rika karbar haihuwa a asibitin.
Hajiya Aisha Sani Wali tace Kwamred Ali Yantandu tun zuwansa ya bai wa harkar lafiya kulawa da muhimmanci duk wani abu da suka nema nan da nan yake zartarwa dan haka ma ya samarda gadaje da sauran kayyakin kulada lafiya kari a wannan Asibiti dan kulada lafiya da karbar masu haihuwa.
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar masu masana,antun hada magunguna
Pharm.Clement Hamidu ya ce sunyi wannan aiki ne dori akan wanda sukeyi a fannoni daban-daban a sassan jaharnan dan inganta ci gaban habakar harkar lafiya.
-
LABARAI19 hours ago
Mun Kamo Wadanda Suka Kai Wa Mawaka Hari A Bauchi, In ji ‘Yan Sanda
-
LABARAI20 hours ago
Na Rike Sana’ata Ta Sayar Da Kankana
-
LABARAI19 hours ago
‘Yan Sanda Sun Gano Sandar Majalisa Da Ta Bace
-
LABARAI19 hours ago
Osinbajo Ya Bukaci A Kyale Matasa Su Yi Takara
-
LABARAI20 hours ago
Yajin Aiki Ya Gurgunta Harkar Lafiya A Asibitin Abuja
-
LABARAI20 hours ago
Bankin Jai’z Ya Kaddamar Da Makarantar Horos Da Ma’aikata A Zariya
-
MANYAN LABARAI19 hours ago
Matasa: Shehu Sani Ya Bukaci Buhari Ya Janye Kalamansa
-
MAKALAR YAU20 hours ago
Kar Mu Zama Butulu A Rayuwa