Connect with us

LABARAI

Shehi Dahiru Bauchi Ya Yi Kira Ga ‘Yan Darika Kan Yin Katin Zabe

Published

on


Jagoran ‘yan Darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Shaihi Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga ‘yan Darika da su gaggauta yin katin zabe kafin zaben da ke tafe a shekarar 2019.

Shaihin Malamin ya bayyana haka ne a wurin taron Maulidin Shehu Ibrahim Nyass karo na 42 da aka gudanar a Abuja ranar asabar din da ta gabata, wanda Darikar Tijjaniyya din ke shiryawa duk shekara.

Shaihi ya bayyana cewa katin zaben shi ne babban makamin da suke da shi wajen zaben duk wanda suke so ya jagorance su.

Ya kuma yi kira ga magoya bayan sa da su yi amfani da katin zabensu yadda ya kamata wajen zaben wanda ke kaunarsu kuma wanda zai kare mutuncinsu, ya yi musu abubuwanda suke so. Ya ce duk wanda ya kai shekarun yin zabe din ya zama wajibi ya yi rajista don ganin ya sami shiga cikin wadanda za su kada kuri’unsu a zaben da ke tafe.

Bauchi ya bayyana cewa wannan maulidi da suke shirayawa, suna shirya ne don tunawa da jagoransu na Afirka, Shaikh Ibrahim Nyass na kasar Sernegal.

Ya ce Nyass ya tallafa sosai wajen ci gaban addinin musulunci a duniya baki daya. Ya kuma bar tarihi sosai a duniyar musulmai. Ya kuma ce sun yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya a kasa da kuma yi mana maganin matsalolin da suka addabemu.

A wajensa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa mabiya Darikar ta Tijjaniyya saboda gudunmawarsu ta addini da kuma addu’ar da suke yi don kawo zaman lafiya a kasa.

Shugaba Buhari, wanda ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa Shaikh Ibrahim Nyass ya ba da gudunmawa wajen ciyar da addinin musulunci gaba a Afirka, Asia da kuma Turai ta hanyar rubuce-rubucensa.

Daga nan ya yi alkawarin cewa Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafawa ayyukan kungiyar don ci gaba da zaman lafiya a kasa.

Ya kuma yi kira ga mabiya Darikar da su ci gaba da yi wa kasa addu’a don samun zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana.

 


Advertisement
Click to comment

labarai