Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Za Ta Amfana Daga Cikin Dala Milyan 770 Na Gidauniyar Hanyoyi

Published

on


Nijeriya ta ce, tana sa ran amfana da taimakon nan na dala 770 na gidauniyar gina hanyoyi domin ta kara karfafa hukumar lura da kan hanyoyinmu, ‘Federal Road Safety Corps,’ da kuma rage hadurran da ke kan hanyoyin namu da kashi 50 ya zuwa shekarar 2030.

Zaunannen Ministan Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Mista Akinremi Bolaji, ne ya bayyana hakan, sa’ilin da yake gabatar da wani jawabin na Nijeriya lokacin kaddamar da gidauniyar a Shalkwatar Majalisar da ke birnin New York.

Bolaji ya ce, “A matsayin ta na kasa mai tasowa, Nijeriya ba tana goyon bayan kafa gidauniyar ce kadai ba, tana ma shaukin sa ran kasancewa cikin kasashe na farko da za su amfana da tallafin.

“Hakan ya zama tilas, domin mu sami damar sanya hannu wajen cimma burin Majalisan na rage hadurran kan hanya da kashi 50.

“Nijeriya ta yi maraba da kaddamarwar, ta kuma alkawarta bayar da cikakken hadin kanta ga wannan gidauniyar.

“Mun tabbata wannan zai kara karfafa hukumarmu ta dogarawan kan hanya, ‘Federal Road Safety Corps,’ wacce ita ce hukumar kasarmu da ke jagorantar lura da kan hanyoyin mu.”

Ya ce, tare da gudummawar dala milyan 770 a kowace shekara na tsawon shekaru 10, hakan zai ceto rayuka milyan biyar ne ya kuma ceci mutane milyan hamsin daga jin raunuka a kasashe marasa karfi da kuma masu tasowa.

“A kokarin da muke yi na ganin mun rage rabin mace-macen da ake samu a kan hanyoyin namu zuwa shekarar 2020, Nijeriya ta tsananta kokarin da take yi a kan hakan.

“A watan Oktoba 2017, Nijeriya ta amince da kafa wata gidauniya da ake sa ran za ta aiwatar da wasu mahimman ayyukan ginawa da duba lafiyar hanyoyinmu, musamman a yankunan karkara da kuma sassan manyan masana’antunmu, masu hanyoyi marasa kyau.

“A shekarar 2018, an kiyasta kashe dala milyan 37 wajen gina wadannan hanyoyin,” in ji Bolaji.

Jakadan na Nijeriya, ya yabawa Taron Majalisar na shirya taro na 82, da zai duba shawarwarin da aka yanke na habaka lafiyr hanyoyi a duniya, ya kara da cewa, Nijeriya ta yi maraba da amincewa da kafa wannan dokan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai