Connect with us

LABARAI

Mun Aminta Da Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada Ya Tsaya Takarar Sanata –Bangis

Published

on


Bayani ya fito cewa, alummar yankin mazabar majalisar dattijai ta Kaduna ta tsakiya (Zone 2) sun aminta da fitowar tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kaduna Alhaji Lawal Sama’ilaYakawada,saboda a halin yanzu babu wanda ya fi shi dacewa da wannan kujerar a yankin, wannan tsokacin ya fito ne daga bakin wani matashin dan siyasa a yankin mazabar majalisar daittijai ta tsakiyar  Kaduna mai suna Bangis Yakawada.

Ya ce, a halin yanzu al’umma daga kananan hukumomi 9 da suka hadu suka yi mazabar majalisar datijjai na Kaduna ta Tsakiya sun nuna bukatarsu suna kuma zawarci da rokon Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada na lallai sai dai fito domin ya yi amfani da kwarewarsa na iya tafiyar da jama’a da iya tattalin tafiyar da mulki wajen da ofishin Sanata a zabe mai zuwa a karkashin jam’iyyar APC.

Bangis Yakawada ya kuma ce, tuni matasa a wannan yankin suka yi nisa wajen tallata kyawawan akidun Alhaji Lawal Samai’ila Yakawa ta hanyar kafa kungiyoyi daban daban domin tattaunawa da fadakar da jama’a irin dimbin alhairin da ke tattare da zabensa a matsayin Sanata, “Kwarewar da Alhaji Lawal Sama’ila ke da shi zai iya rike kujera shugaban kasa, babu wani matsayi a fagen siyasa da ba zai iya rikewa ba saboda kwarewarsa” inji shi.

Ya kara da cewa, matasa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa daga dukkan jam’iyyun siyasa dake yankin mazabar majalisar dattijai na Kaduna ta Tsakiya sun hada kansu ba tare da muna banbancin siyasa ba na ganin sun mara wa wannan burin a ganin Alhaji Lawal sama’ila Yakawada ya fito takarar wannan kujera ta Sanata na Zone 2, a saboda haka ya mika rokonsa ga Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada daya amsa kiran al’umman na zone 2 na ya fito takara saboda amincewa da sallamawa da al’umma suka yi masa.

Bangis Yakawada ya kuma nuna cewar, yana da tabbacin rikicin da jam’iyyar APC ke fuskanta a ‘yan kwanakin nan abu ne da za a warware kwanan nan, a kan haka ne ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar dasu rungumi akidar sulhu domin a samu nasara a zabbukan da suke tafe.


Advertisement
Click to comment

labarai