Connect with us

WASANNI

Muhammad Salah Ya Karya Tarihin Drogba A Gasar Firimiya

Published

on


Mohamed Salah ya karya  tarihin da tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya kafa a gasar firimiya na kasancewa dan wasan Afirka da ya fi cin kwallo a kaka daya, bayan da ya zura kwallo daya daga cikin kwallo uku da Liberpool ta doke Bournemouth.

Drogba ya yi bajintar cin kwallaye 29 a kaka daya a gasar ta firimiya, to amma kuma kwallon  da Salah ya ci a wasan na ranar Asabar ta zama ta 30 da ya ci a kakar nan, abin da ya sa ya wuce tsohon dan wasan na Chelsea wanda ya yi tasa bajintar a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010.

Nasarar ta sa Liberpool ta ci gaba da zama a matsayi na uku akan tebur amma yanzu maki daya ne kawai tsakaninta da ta biyu wato Manchester United.

Masu masaukin bakin sun fara wasan da kyau inda Sadio Mane ya fara zura kwallo a raga minti bakwai da shiga fili.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 69 Salah ya ci ta biyu, wadda ta ba shi damar zama na daya a ‘yan wasan Afirka da suka fi cin kwallo a kaka dayar a firimiya, kuma ta 40 da ya ci wa kungiyar a dukkanin gasa a kakar nan.

Kwallon  ta sa ya zama ta farko da ya yi wannan bajinta a Liberpool tun bayan Ian Rush a kakar 1986-87. Inda shi ma ya ci wa kungiyar kwallo 40 a kaka daya.

Roberto Firmino ne ya ci wa kungiyar kwallo ta uku, wadda ta kasance ta 15 da ya ci a gasar firimiya a bana, kuma ta tabbatar da nasara ta biyar da kungiyar ke yi a jere a wasa shida.

Mai koyar da yan wasan Liberpool Jurgen Klopp wanda ya ce yawan kwallon da suke ci a bana abin kamar hauka, ya ce duk wani korafi da ake yi a kan Salah da suka sayo daga Roma a bazarar da ta wuce a kan fam miliyan 34 a yanzu ya kau.

 


Advertisement
Click to comment

labarai