Connect with us

KASUWANCI

Miyetti Allah Ta Hada Kai Da Kamfanin Sadarwa Na GLO Don Gano Shanun Da Aka Sace

Published

on


Kamfanin sadarwa na GLO, ya kaddamar da wata na’ura ta gano inda shanu suke, domin amfanan Fulani makiyaya a kasarnan, suka ce za su yi aiki tare da kungiyar makiyaya ta, ‘Miyetti Allah Kautal Hore,’ domin samun nasarar sabuwar fasahar.

Da yake tattaunawa da manema labarai, a wajen wani taron karawa juna sani da aka shirya a Auta-Balefi, da ke Karamar Hukumar Karu, Jihar Nasarawa, Manajan kasuwanci na kamfanin na GLO, Philip Crown-Adedoyin, ya zayyana amfanin sabuwar na’urar ta fasahar gano inda shanu suke, da hakan zai rage yawan satan shanayen, da hadarin kiwo da sauran su.

A cewar Mista Adedoyin, Fulani makiyaya da za su yi aiki da fasahar, za su sami mafita nan take kan inda gano shanayen na su ta hanyar wasu na’urori da za a makala masu a wuyayen su  domin lura da wuri da kuma yanayin da suke ciki.

Ya ce nan gaba, Fulani makiyaya za su iya sanin matsayi da lafiyar shanun na su ke ciki, da kuma cutukan da ke addaban su gami da gano inda suke da kuma inganta fitar da naman dabbobin zuwa kasuwannin waje.

Da yake yabawa kamfanin na GLO, kan wannan sabuwar fasahar da ya kirkiro, Shugaban kungiyar ta, ‘Miyetti Allah Kautal Hore,’ Bello Abdullahi Badejo, cewa ya yi, zai fara gwajin na’aurar kan shanayen sa.

Ya ce, gano inda shanu suke, zai magance matsalolin satan shanu a kasarnan, sai ya kirayi gwamnati da ta tallafawa shirin.

Shugaban kungiyar na kasa, ya yi roko ga kamfanin na GLO, da ya saka matasan Fulani masu ilimi wajen habaka wannan sabuwar fasahar, domin ta samu isa ko’ina.

Shi ma da yake magana a wajen taron, Sakataren kungiyar ta, ‘Miyetti Allah Kautal Hore,’ yabawa kamfanin na GLO, ya yi, kan samar da wannan fasahar, ya ce, za su fara gwada ta da shanun shugaban kungiyar na su, sannan kuma daukacin Fulani makiyaya da suka halarci taron duk za su jarraba wannan sabuwar fasahar.


Advertisement
Click to comment

labarai