Connect with us

MAKALAR YAU

Me Karfi Ya Tsira… Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Spencer

Published

on


0703 666 6850

Yallabai, duk da ina sane sarai, cewa ba ka numfasawa a doron kasa, kuma babu wata duriyarka ko birbishin nazariyyarka; amma na san da sauran rina a kaba, saboda wadanchan nazarori da rubuce – rubucen da ka yi a karni na 19 su na nan, su na bibiyan rayuwarmu, sun hana mu sakat.

Ba zan ce ka yi wa duniya da al’umma illa ba, saboda turawan Yamma sun morewa nazariyyarka, sun ci ribarka, sun karu matuka da zantukanka. Musamman yadda ka halasta musu muguwar dabi’ar jari hujja, dabi’ar danniya da mugunta tsantsa.

Kar ma ka fara tunanin cewa ni dan akidar ‘Mardist’ ne, ba wannan ba ne dalilan wannan wasikar. Kasata Nijeriya ce na yi wa kallon tsaf, na rasa da me zan nazarce ta, na karance ta, sannan na kwatanta idan ba da nazariyyarka ba. Tunani da fikirorinka sun jefa mu a cikin wani hali, babu abin da ke faruwa a kasarmu da ya wuce mai karfi ya tsira, shi kuma marar karfi ko oho ‘Surbibal of the fittest’.

A lokacin da na ke karatu, a dai dai tarihin rayuwarka, sai na yi karo da wani abu da ya bani mamaki. Wurin da na ga cewa a gidanku an haifi ‘ya ‘ya 9, amma kai kadai ne ka tsira da rai har ka girma a cikin wadannan ‘ya ‘ya. Dukkansu su na kanana su ka mutu. Sai mai nakaltowa ya ce, wannan na daga cikin dalilan da su ka sa ka kirkiri nazariyyar ‘Mai Karfi ya tsira, Marar karfi ko oho’ a turance ‘Surbibal of the Fittest’.

Da ma kowanne manazarci, marubuci da kuma masani, babban ma’aunin da a ke amfani da shi wurin fahimtar dalilan nazarinshi shi ne tarihin rayuwarshi, tarihin al’umman da ya taso a cikinta, da kuma abubuwan da su ka faru a rayuwar yau da kullum a lokacin da ya ke raye.

Haka kuma tarihi ya adana cewa Spencer ba ka taba zuwa makaranta ba, duk da kuwa mahaifinka da Kawunka sun koyar da kai a gida. Kuma a wadannan ‘yan karance – karancen na koyarwan gida, an ce ka fi son lissafi ‘Mathematics’. Don haka ko da ka soma rubuce – rubuce a bangarorin ‘Biology’ da ‘Pyschology’, sai na yi tunanin za ka rika yi ka na lissafin dai dai, da ba dai dai ba. ba kawai domin jin dadin mutanen nahiyar Turai ba, sai don gudun irin masifun da nazarinka ya jefa mutane a ciki a yau.

Idan da ka na da kwarewa a fannin kimiyya irin wacce Auguste Comte ya samu a makarantar ‘Ecole Polytechnikue’, da ba ka saki layi kamar yadda ka yi a nazarin ‘Mai Karfi ya tsira, marar karfi ko oho’ ba. Ko ba komi, duk da akwai wasu gyare – gyare da kuma kura – kurai a nazariyyar Comte, amma dai amfanoninsu a cikin al’umma a yau, sun zarce naka. Kuma shi ya gode Allah, ba a kama shi dumu – dumu da satar fasaha ba, kamar yadda a ka kama ka da satar sunan ‘Social Statics’ daga aikin Comte ‘Positibe de Philosophie’, wanda Harriet Martineu (Mace ta farko a kimiyyar zamantakewa) ta fassara daga Farasanchi zuwa Ingilishi.

Wadansu na yi ma kallon ‘Conserbatibe’, wanda a hakikanin gaskiya a farkon rayuwarka ka fi kama da ‘Political Liberal’. Daya daga cikin dalilan da ya sa a ke danganta ka da ‘Liberal’ shi ne ra’ayinka na ‘Laissez – Faire’. Ra’ayin da ya yi wa wasu dadi sosai a nahiyar Turai, ya sa masu karfi su ka yi ta cin karnukansu babu babbaka, su kuwa marasa karfi a ka barsu a banzance, ko oho.

Ra’ayinka na ‘Laissez Faire’ da ke cewa babu bukatar hukuma ta tsoma baki a cikin lamurra da harkokin jama’a, sai dai kawai a lamurran da su ka shafi samar da tsaro ga rayuka da dukiya; amma fa babu batun bayar da taimako ga mabukata, tallafi ga gajiyayyu da nakassasu. Mafi muni ma da ka ke ganin cewa wai babu bukatar gwamnati ta yi ayyukan kawo daidaitu a rayuka da shiga tsakani.

Ka ce, ita duniya ta na bunkasa ne a kashin kanta, rayuwa na yalwata ne ba tare da an kawo wani taimako ko agaji na musamman ba. A rabu da kowa ya yi sha’aninsa, iya ka wayonka da karfinka iya nasararka. Kuma wai ka ce, idan kuma a ka ce sai an taimaka ko an sa hannu a lamurran mutane, abubuwa za su gurbace ne, maimakon su daidaita.

Mafi muni na daga ra’ayoyinka, kuma wanda ya fi cutar da mutanen Afrika, mutanen Nijeriya ma dai, shi ne nazarin ‘Mai Karfi ya Tsira, Marar karfi ko oho’ a turance ‘Surbibal of the Fittest’. A cewarka, kamar yadda tsirai da dabbobi su ke walwala su rayu, haka ma mutane su ke yi. Idan har hukuma ba ta sa hannu a lamurran mutane ba, masu karfi ne za su tsira kuma su habbaka, a yayin da marar karfi kuma za su ruguje su zama tarihi. Wannan ra’ayi na mugunta da keta, kuma ra’ayin kin talakawa da marasa karfi, babu zuciyar da za ta aminta da shi sai muguwar zuciyar ‘yan jari hujja.

Duk da a yanzu a duniya babu wata makaranta ko fahimta wacce ta ke tinkaho da koyarwanka, sunanka ma ba don a sakamakon tarihi ba, da tuni an shafe shi. Hatta a nahiyar Turai, an sauka a layin waccan fahimtar ta ka, hukuma na taimakon marasa shi, sannan kunciyoyi da cibiyoyi na tallafawa ba ma a nahiyarsu ba kadai, har a sauran nahiyoyin duniya da a ke fama da talauci.

Duk yadda a ka yi, masu kudinmu a Nijeriya, da kuma hukumominmu, su na amfani ne da gurgun nazarinka na ‘Surbibal of the fittest’, bisa la’akari da yadda masu kudi, ‘yan siyasa, da masu karfi ne kawai ke tsira, su kuwa raunana, talakawa, da nakassasu ko oho. ‘yan siyasa su saci kudin gwamnati, masu kudi su cuci ma’aikata, masu karfi kuma su yi sata da fashi da makami, duk dai domin su dace da ra’ayinka na Mai karfi ya tsira, marar karfi ko oho.


Advertisement
Click to comment

labarai