Connect with us

LABARAI

Matan Chibok: Fadar Shugaban Kasa Ta Mayar Wa Salkida Martani

Published

on


Ofishin shugaban kasar Nijeriya ta ce, bayanin nan da dan jarida Ahmed Salkida, ya yi a kafar sadarwa ta Twiter na cewa wasu daga cikn ‘yan matan Chibok da aka sace sun mutu, bayani ne da gwamnatin shugaba Buhari bata da shi a hukumance.

A na da yakinin cewar, Mista Salkida nada kusanci na musamman ga kungiyar Boko Haram, kungiyar da tayi garkuwa da ‘yan mata 217 daga makarantar GSS Chibok a shekarar 2014.

Yayin da aka riga aka tsirar da dayawa daga cikin ‘yan matan ta hanyar yarjejeniya da ‘yan Boko Haram din wasu kuma tuni suka gudu daga inda ake tsare dasu yayin da fiye da ‘yan mata 113 suke hannun su har yanzu.

A wani sakonnin Twiter da Mista Salkida, ya watsa ranar Asabar da tayi dai dai da shekara 4 da sace ‘yan matan yace, ‘yan ,mata 15 ne kawai ked a rai a cikin wadanda suka rage.

Ya ce, majiyarsa daga cikin kungiyar ta Boko Haram ta bayyana masa cewar sauran sun mutu ne a hare jaren da sojojin Nijeriya suka yi kai wa ne a lokuttan baya.

Da jami’an gwamnatin tarayya ke maid a martini sun ce bayanan da Mista Salkida ya yi babu a cikin bayanan da gwamnati ked a shi a hakin yanzu.

Gwamnati ta kara da cewa, basu samu irin wannan bayanan daga wadanda suka ksace ‘yan matan ko kuma kungiyoyin kasa da kasa da suke hulda dasu.

Jami’in watsa labaran shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sako daya aika wa PREMIUM TIMES, y ace, bas u taba sanya Mista Salkida a kokarin karbo ‘yan matan Chibok 100 da aka yi a baya ba, kuma har a aka mayar dasu ga iyalansu.

Mista Shehu basu sanya dan jaridar cikin kokarin sakin ‘yan matan ba a wannan karon.

“In ma akwai wani bayani daya ke dasu gae da ‘yan matan Chibok to har yanzu bai tuntubi gwamnatin Nijeriya da wannan bayanin ba”

“Saboda haka duk wani neman karin bayani da kuke nema kuna iya gabatar dasu ga Mista Salkida,” inji Mista Shehu

Ya kara da bayanin cewar, bayanan dake hannun gwamnati da kungiyoyin kasashen waje na karfafa su wajen ci gaba da neman ceto sauran ‘yan matan Chibok, ba zasu yi kasa a gwiwa ba domin ganin haka.

 


Advertisement
Click to comment

labarai