Connect with us

LABARAI

Lambar Yabo Ta ZIK: An Karrama Gwamna Masari A Legas

Published

on


Gidauniyar tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Nmandi Azikiwe ta shirya taron karrama wasu daga cikin fitattun mutane da suka bada gudunmawa a cigaban al’umma acikin shekarar 2017 ciki harada Gwamna Masari, bayan wani bincike da wata cibiya mai suna ‘’Public Policy Research And Analysis Center’’ da ke jihar Legas.

Da man dai wannan cibiya ta saba gudanar da lakca duk shekara domin bayyana wasu daga cikin halayyar marigayi Dakta Nmandi Azikiwe da kuma tunawa da wasu abubuwan da ya bari. Daga baya kuma cibiyar suka yi tunanin bullo da bada kyauta ta musamman ga wasu kebabun mutane da suka taka mahimmiyar rawa wajan cigaban al’umma.

ita dai wannan karramawa da aka yi wa gwamna Aminu Bello Masari tare da wasu manyan mutane da suka bada gudunmawa ta fannoni daban-daban ta biyo bayan wani bincike na musamman na wata cibiyar bincike da tsare-tsare da kuma yin fashin baki ta gudanar inda daga karshe ta bayyana gwamna Masari a matsayin gwamnan da ya kawo canji a fannoni da dama da suka hada da kawo cigaba a rayuwar jama’a da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen jihar Katsina.

Cibiyar ta kara da cewa Masari ya dage kai da fata wajan ganin martabar jihar Katsian ta dawo a idon duniya, ta ce wannan kokari na shi ya zuwa yanzu ya fara haifar da da mai ido, kuma jama’a tuna suka fara yin alkalanci akan wannan cigaba da ya kawo.

A wannan cibiya Ferfesa Jibrin Aminu shi ne baban mai bada shawara sai kuma shugabanta wanda yake sanan ne ne, wato Cif George Obiozora wadanda dukkaninsu masana ne game da yadda ake zaban mutun wanda ya bada gudunmawa kafin a ba shi wata kyauta ko girmamawa, wannan yana daga cikin abubuwan da gwamna Masari ake yawan yin masa tambihi akan sa.

Wasu daga cikin wadanda za a karrama wajan  wannna gaggarumin biki sun hada daa gwamna Aminu Belo Masari na jihar Katsina da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi II da gwamna jihar Ribar Barrister Nyeson Wike da Cif Audu Ogber Ministan ayyukan Gona na tarayyar Najeriya da kuma Mista Ernest Ebi shugaban Banki Fidility.

Sauran sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar ACN Cif Adebisi Akende da Babban Darakta a ma’aikatar NNPC Dakta Mai Kanti Baru da Dakta Adedeji Adeleki shugaban kamfanin Pacific Holding Limited da uwargidan gwamnan Anambra Cif Ebelechukwu Obiano da Uwargidan gwamnan Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar

Daga cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen akwai gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar, da gwamnan jihar Sakwato, Aminu Waziri Tambuwal, haka kuma an samu wakilinci masu martaba sarakunan Katsina da kuam Daura wadanda ‘ya ‘yan su suka wakilta a wajan wannan taro.

Kasaitaccen bikin wanda aka shirya shi a cibiyar Cibic da ke rukunin unguwanin bictoria Inland da ke jihar Legos ya samu halartar dubbin magoya bayan gwamna Aminu Bello Masrai daga jihar Katsina da suka hada da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu rike da mukamai a gwamnatace.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro na tarihi sun hada da mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu da Sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammaed Inuwa da ‘yan majalisar Dattawa da ‘yan Majalisar wakilai da kuma ‘yam majalisar dokoki ta jihar Katsina da sauran su.

Akwai mutane irin  su babban alkalin alkalai  mai Shari’a Musa Abubakar Danladi da shubana kamfanin Mad air Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alahji Shitu S Shitu da sauran manyan masu fada ajitare da shuganan Jam’iyyar APC na kasa mista Jonh Oyegun

 


Advertisement
Click to comment

labarai